Shekaru 65 da ‘yanci: Daga yanzu wahala ta ƙare – Tinubu

Spread the love

*Cikin shekaru biyu mun samu gagarumin cigaba, inji Shugaban ƙasa

*Yunwa na kashe ’yan Nijeriya, amma ko a jikin Tinubu – Atiku

*Kada ku yanke ƙauna da cigaban ƙasa – Jonathan ga ‘yan Nijeriya

*Akwai buƙatar kishin ƙasa da haɗin kan al’umma, inji Sarkin Kasuwar Beirut

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce, gwamnatinsa ta samu gagarumin cigaba a fannoni daban-daban cikin shekaru biyu da suka gabata, duk da ƙalubalen tattalin arziki da tsaro da ƙasar ta fuskanta.

A jawabin da ya gabatar yayin bikin cikar Nijeriya shekaru 65 da samun ’yancin kai, Shugaba Tinubu ya ce, manufofi da matakan da aka ɗauka sun fara sauya akalar tattalin arzikin ƙasar.

ƙaruwar kuɗaɗen shiga da rage bashi:

Shugaba Tinubu ya bayyana cewa gwamnati ta samu ƙarin kuɗaɗen shiga daga albarkatun da ba na man fetur ba, inda a bana kaɗai aka tara fiye da Naira tiriliyan 20. A cewarsa, adadin da ake kashewa wajen biyan bashin da ake ci ya ragu daga kusan kashi 97 zuwa ƙasa da 50.

Farfaɗowar tattalin arziki

Rahoton Hukumar ƙididdiga ya nuna cewa tattalin arzikin Nijeriya ya samu ƙaruwar kashi 4.23 a zango na biyu na shekarar 2025, wanda ya zarce hasashen IMF na kashi 3.4. Haka kuma, hauhawar farashin kayayyaki ya sauka zuwa kashi 20.12 a watan Agusta, mafi ƙaranci cikin shekaru uku.

Cigaban masana’antu da kasuwanci:

Shugaban ƙasar ya ce, Nijeriya ta koma “net eɗporter”, wato tana sayar da kaya ga ƙasashen waje fiye da yadda take saya daga garesu. A cewarsa, kayayyakin da aka ƙera a gida Nijeriya sun ƙaru da kashi 173, kuma kusan rabin abin da ake fitarwa yanzu ba man fetur ba ne.

Ya ƙara da cewa samar da ɗanyen mai ya ƙaru daga ganga ƙasa da miliyan ɗaya a rana a shekarar 2023 zuwa ganga miliyan 1.68, yayin da a karon farko cikin shekaru 40 aka fara tace man fetur a cikin gida.

Asusun ajiyar ƙasa da darajar Naira:

Shugaba Tinubu ya ce, asusun ajiyar ƙasar ya ƙaru zuwa dala biliyan 42.03, mafi girma tun 2019. Ya kuma ce Naira ta farfaɗo bayan rikicewar da ta shiga a 2023–2024, inda giɓin farashin gwamnati da na kasuwar bayan-fage ya ragu sosai.

Shirye-shiryen tallafi ga talakawa:

Gwamnati ta raba Naira biliyan 330 ga iyalai miliyan takwas a ƙarƙashin shirye-shiryen tallafin zamantakewa. Haka kuma, matasa sama da 153,000 sun amfana da lamunin Credicorp, yayin da ɗaruruwan dubban ɗalibai suka samu lamunin karatu a ƙarƙashin shirin tallafin NELFUND.

Ababen more rayuwa:

A ɓangaren gina ƙasa, gwamnati ta ce ta ci gaba da manyan ayyuka kamar layin dogo na Kaduna–Kano da Kano–Katsina–Maraɗi, titin Legas–Kalaba Coastal Highway, da kuma titin Sakkwato–Badagry.

Tsaro:

Shugaban ya ce jami’an tsaro na ci gaba da nasara a yaƙi da Boko Haram a Arewa maso Gabas da IPOB a Kudu maso Gabas. Ya ce zaman lafiya ya fara dawowa a wasu sassan da rikice-rikice suka daɗe suna addaba.

Matasa da ƙirƙire-ƙirƙire:

Tinubu ya jaddada cewa gwamnati na cigaba da zuba jari a matasa ta hanyar shirye-shiryen inganta ƙirƙire-ƙirƙire da fasaha, ciki har da shirin iDICE programme, wanda zai tallafa wa masu fara sana’o’i ta intanet da ƙere-ƙere.

“Lokacin sabuwar Nijeriya ya zo”:

Shugaban ya ce duk da raɗaɗin da ’yan Nijeriya suka fuskanta sakamakon gyare-gyaren tattalin arziki, sakamakon ya fara bayyana.

“Ina tabbatar muku da cewa lokaci ya yi da Nijeriya za ta zama ƙasa mai dogaro da kanta, mai arziki, da alfahari da kanta,” inji shi.

Yunwa na kashe ’yan Nijeriya, amma Tinubu ko a jikinsa – Atiku:

Tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya yaba wa ’yan Nijeriya bisa abin da ya kira ‘haƙurinsu, juriya da ƙwazo’ duk da tsananin matsin tattalin arziki da rashin tsaro da suke fama da shi.

A cikin saƙonsa na murnar cikar Nijeriya shekaru 65 da samun ’yancin kai da ya aike ga ’yan ƙasa, Atiku ya zargi gwamnatin jam’iyyar APC da watsi da al’umma, yana mai cewa sun bar ’yan Nijeriya su fama da rayuwa mai cike da ƙalubale ba tare da kulawa ba.

Atiku ya ce “’yan Nijeriya na fama da tsananin rashin tsaro, karancin abinci, rashin aikin yi da kuma yanayi mai cike da fargaba da rashin kyakkyawar makoma wanda ya kara muni sakamakon rashin tausayi da rashin kulawar gwamnatin APC.

“Abin takaici ne cewa a cikin kasa mai albarka da arziki, miliyoyin mutane sun koma ’yan gudun hijira da mabarata a cikin kasarsu. Kowace gwamnati mai kishin kasa tana daukar rayuwa da tsaron ’yan kasa da muhimmanci.

“Amma abin da muke fama da shi a yau shi ne gwamnatin da ta watsar da jama’arta. Yunwa na kashe ’yan Nijeriya, ’yan bindiga na hallaka al’umma, amma Shugaba Bola Tinubu da ministocinsa suna kallon abubuwa suna faruwa ba tare da nuna damuwa ba.”

Sai dai Atiku ya buƙaci ’yan kasa da kada su yanke kauna, yana mai tunatar da su cewa shekarar 2027 na tafe da damar sauya shugabanci mara nagarta da kuma dawo da rayuwa mai kyau.

“Kyawun dimokuraɗiyya yana cikin ikon kada ƙuri’a. Ko da kuwa jama’a na cikin ƙunci da zalunci a yau, za su samu damar kawar da wannan gwamnati mara iya aiki a zaɓe mai zuwa. Wannan iko ne da babu wata ƙungiya da za ta iya ƙwacewa daga hannun jama’a,” inji shi.

A cewarsa, duk da cewa Nijeriya ta cika shekara 65 da samun ’yancin kai, har yanzu tana tafiyar hawainiya sakamakon shekaru da dama na shugabanci mara nagarta da almubazzaranci.

Jonathan ya hori ‘yan Nijeriya da kada su yanke ƙauna da ci gaban ƙasa:

Tsohon Shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, ya roƙi ‘yan Nijeriya da kada su yanke ƙauna duk da ƙalubalen da ake fuskanta a yanzu, sai dai su ci gaba da riƙe fata a kan manyan damarmaki da ke cikin ƙasar.

Jonathan ya bayyana hakan ne a cikin saƙon taya murna ga ‘yan Nijeriya a bikin cikar ƙasar shekaru 65 da samun ‘yancin kai.

Saƙon ya fito ne daga hannun mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Mista Okechukwu Eze, a Abuja ranar Laraba.

A cewar Jonathan, bikin ranar ‘yancin kai na ba da dama ga Nijeriya ta waiwayi tafiyarta ta gina ƙasa, ciki har da ƙalubalen da aka fuskanta da kuma manyan damarmaki da ke gaba.

“Nijeriya ƙasa ce mai albarka, wadda Allah ya ba da yalwar ƙasa, albarkatun ƙasa, kuma sama da komai, basira da ƙirƙira na al’umma.

“ɗumbin al’adunmu da iliminmu da hikimarmu sun ci gaba da bambanta ‘yan Nijeriya a kowane fage na rayuwar ɗan adam, a gida da wajen ƙasa.”

Jonathan ya shawarci ‘yan Nijeriya da su bar kishin ƙasa ya jagoranci ayyukansu.

Akwai buƙatar kishin ƙasa da haɗin kan al’umma — Sarkin Kasuwar Beirut:

Mai girma Sarkin Kasuwar Beirut ta siyar da wayoyi a birnin Kano, Alhaji Muhammad Inuwa Labaran, ya bayyana cewa, cikar Nijeriya shekaru 65 da samun ’yancin kai ya zo da canje-canje masu yawa, wasu na cigaba, wasu kuma akasin haka.

Ya ce, babban abin da ake buƙata yanzu shi ne shugabanni masu kishin ƙasa, masu adalci da tsoron Allah, waɗanda za su jagoranci kawar da ƙabilanci da mummunar siyasa tare da haɗa kan al’umma duk da bambance-bambancen addini da al’adu.

A cewarsa, Nijeriya tana buƙatar shugabanni nagari da al’umma masu bin doka da oda, riƙon amana da kyakkyawar mu’amala a sana’o’i da harkokin rayuwa. Ya yi fatan Allah ya kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali a Kano, Nijeriya da duniya baki ɗaya.

By ukarofi