Yan bindiga sun sace kansiloli biyu a Zamfara

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

A ranar Laraba ne wasu ‘yan bindiga suka sace wasu kansilolin ƙaramar hukumar Maradun guda biyu a Zamfara.

Rahotanni sun nuna cewa an yi garkuwa da Kansilolin guda biyu masu wakiltar Gidan Goga da Tsibiri a ƙaramar hukumar Maradun a Unguwar Mareri da ke Gusau babban birnin jihar.

Wakilinmu ya ruwaito cewa an yi garkuwa da Kansilolin biyu ne a ƙofar gidajen su dake unguwar ta Mareri da misalin karfe 6:50 na yammacin ranar Laraba.

A yayin da Wakilin mu ya tuntuɓi jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar DSP Yazid Abubakar ta wayar tarho, ya tabbatar da faruwar lamarin.

A cewarsa, rundunar ta tura jami’anta da ke yaƙi da masu garkuwa da mutane zuwa yankin domin gano waɗanda suka aikata laifin.

Ya kuma ƙara da cewa, ana kan ƙoƙarin kuɓutar da kansilolin da aka yi garkuwa da su da Kuma tabbatar da an kamo waɗanda suka aikata laifin.

Ya buƙaci mazauna garin Gusau da su riƙa taimakawa da bayanai masu amfani kan duk wani baƙon ido da ba su aminta da shi ba don ɗaukar matakin gaggawa daga rundunar ƴan sandan jihar.

By ukarofi