NNPC ya rattaɓa hannu kan yarjejeniya ta samar da ɗanyen mai da Matatar Dangote

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Kamfanin Man Fetur na Nijeriya (NNPC) ya ƙulla sabuwar yarjejeniya ta samar da ɗanyen mai da matatar man Dangote, inda zai ƙara samar da man na tsawon shekaru biyu a wani mataki da ake sa ran zai ƙarfafa shirin Gwamnatin Tarayya na “ɗanyen mai Naira”.

Yarjejeniyar wacce aka kammala a watan Satumba, kamfanin mai na gwamnati zai samar wa matatar mai ƙarfin tace ganga 650,000 a kowace rana kago biyar-biyar na ɗanyen mai a watan Satumba da Oktoban 2025, a cewar kakakin NNPC, Andy Odeh. Odeh, wanda ya tabbatar da tsarin a cikin martanin saƙon rubutu ga tambayoyin Bloomberg.

Da wannan sabon tsari, jimillar zanyen man da ake samarwa matatar man Dangote a yanzu ya kai ganga miliyan 82 tun daga watan Oktoban 2024, inji NNPC, inda ya bayyana cewa kashi 60 cikin 100 na kayan da ake sayarwa duk a Naira ne.

A shekarar da ta gabata, Nijeriya ta ƙuduri aniyar samar da gangar ɗanyen mai 445,000 a kowace rana ga matatar a cikin kucin gida. An tsara manufar ne don rage matsin lamba na musayar kuɗaɗen waje a kan Naira, daidaita farashin famfun mai, da zurfafa aikin tace mai a cikin gida.

Jami’an gwamnati sun yi nuni da cewa, shirin, idan ya yi nasara, za a iya faɗaɗa shi zuwa sauran matatu ‘yan asalin ƙasar.

Wannan ci gaban dai na zuwa ne a daidai lokacin da matatar man Dangote ta koma sayar da mai a  Naira a ranar Asabar ɗin da ta gabata, biyo bayan tsoma bakin shugaban kwamitin fasaha na ɗanyen mai na Naira. A cikin saƙon da ta aikewa kwastomominta, matatar ta sanar da cewa, “Bayan shigar da Naira ga shugaban kwamitin fasaha na ɗanyen mai, muna farin cikin sanar da ku game da sake dawo da sayar da man fetur a Naira wanda zai fara aiki nan take.”

Sake dawo da shi wani muhimmin ci gaba ne ga ƙoƙarin gwamnatin tarayya na ƙarfafa hada-hadar kuɗaɗen cikin gida a ɓangaren mai.

Masu sa ido a masana’antu sun ce haɗin gwiwar da ke tsakanin NNPCPL da matatar Dangote ya nuna wata dabarar da za a cimma nasarar samar da wadataccen makamashi

A farkon watan Mayu, Dangote da kansa ya jaddada cewa matatarsa ​​da kuma kamfanin mai na ƙasa ba abokan gaba ba ne illa abokan hulɗa ne.

“Babu wata gasa a tsakaninmu, ba mu zo nan don yin gogayya da NNPC ba, NNPC na daga cikin harkokin kasuwancinmu, kuma mu ma muna cikin NNPC. Wannan zamani ne na haɗin gwiwa tsakanin ƙungiyoyin biyu,” inji Dangote yayin ziyarar ban girma da ya kai wa Babban Daraktan Rukunin NNPC, Bashir Bayo Ojulari, a Abuja.

Manazarta na ganin sabuwar yarjejeniyar samar da ɗanyen man ta shekaru biyu ba wai kawai amincewa da matatar man da Dangote ya samar na dalar Amurka biliyan 20 ba, har ma wata alama ce ta ƙudirin gwamnati na ɗorewar manufar ‘ɗanyen mai a naira’ a matsayin wani tsari na dogon lokaci na kare kuɗaɗen gida da kuma daidaita kasuwar man fetur.

By ukarofi