Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Hukumar Kula da Tsarin Fansho ta ƙasa (PTAD) ta sanar da fara aiwatar da ƙarin kuɗaɗen fansho da aka amince da shi kwanan nan ba jimawa.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata, hukumar ta ce, karin N32,000, ga masu karɓar fansho da suka cancanta, an tabbatar da shi ne a cikin tsarin biyan fansho na watan Satumba na 2025.
A cewar PTAD, ci gaban ya biyo bayan fitar da wani ɓangare na naira miliyan 420.188 daga cikin kuɗaɗen gaggawa na Naira Biliyan 45 da shugaba Bola Tinubu ya amince da shi a baya.
“Wannan muhimmin al’amari ya sake tabbatar da himmar Gwamnatin Tarayya a fili don kiyaye walwala da haƙƙin ’yan fansho da ke ƙarƙashin shirin (DBS) bisa ga manufar sabunta fata,” inji Daraktan PTAD.
Mahukunta PTAD sun nuna jin daɗinsu ga shugaba Tinubu kan amincewa da tallafin gaggawar, wanda a cewarsu hakan zai inganta jin daɗi da walwalar masu karɓar fanshon.
