
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Cibiyar kula da hada-hadar kuɗaɗe ta bankuna a Nijeriya (NIBSS) tana shirin samar da sauyi a harkar hada-hadar kuɗaɗe a ƙasar wajen soke cajis da ake yi wa kwastomomin banki ƙarƙashin tsarin NIP.
Darakta Manaja na Cibiyar Premier Oiwoh ya sanar da haka a ranar Alhamis yayin babban taro na ‘Globus Bank Fintech Summit 2025’ a Legas, inda ya gabatar da lakca mai taken ‘From Cashless to Smart Economies: Shaping the next Frontier of Financial Innovation.’
Ya bayyana cewa, gyaran zai fara aiki ne a shekara mai zuwa, wanda zai sauya tsarin cajis ɗin daga fee-per-transaction zuwa subscription-based, wato daga cazar kuɗi ga kowane hada-hadar tura kuɗi zuwa rajista na wani zango.
A cewarsa, za a yi hakan ne da nufin bunƙasa tsarin biyan kuɗi na dijital, wanda ya bayyana a matsayin mafi girman gasa a masana’antar harkokin banki.
Ya kuma ce, hakan zai taimaka wajen zamanantar da tsarin da inganta gudanarwarsa gami da toshe ƙofofin damfara a asusun bankunan kwastomomi.
Daraktan ya ƙara da cewa, hakan abu ne da zai sa tsarin hada-hadar kuɗaɗe a bankuna ya dace da na sauran ƙasashen duniya, waɗanda da dama tuni suka samar da ci-gaban a harkokinsu.
