Babu rushe cancantar ƴan takara ko jam’iyyu a ƙudirin dokar zaɓe da ake neman tabbatarwa – IJAP

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Tawagar tabbatar da gaskiya da adalci ta shari’a (IJAB) ta gano cewa neman a rushe cancantar ƴan takara da jam’iyyun siyasa saboda manyan laifuka ba sa cikin ƙudirin zaɓe na 2025 da ake ƙoƙarin tabbatarwa.

Shugaban IJAB Mai Shari’a Mojeet Adekunle Owoade ya bayyana haka a yayin taron IJAP karo na uku ƙarƙashin ‘CiTi-Act Projet of ActionAid Nigeria’ (AAN) a Abuja.

An gudanar da taron ne ranar Juma’a, wanda ya ƙunshi tsokaci da warware wasu al’amura da suka janyo cecekuce acikin al’umma.

Ya bayyana cewa akwai hukunta masu laifin zaɓe acikin ƙudirin, waɗanda su ma sun gamsu da haka, inda ya bada misali da sashen da suka nemi ƙari akan tarar mallakar katin zaɓe sama da ɗaya, rashin amfani da katin yadda ya dace.

Haka kuma akwai, miƙa jaddawalin sunayen ƴan takara ba yadda aka tsara ba, haura kashe-kashen kuɗaɗe sama da yadda aka amince, miƙa takardun bogi da makamantansu.

By Babaji