
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Sanannen tauraro kuma mawaƙin Nijeriya, Innocent Idibia da aka sani da 2Baba, ya musanta jita-jitar kama shi a Birtaniya bisa zargin samun tsama da matarsa, Natasha Osawaru, wadda ƴar majalisa ce a Majalisar Dokokin Jihar Edo.
An fara yaɗa jita-jitar ne bayan da aka ga 2Face bai halarci gabatar da wasa ba a tafiyarsa ta ‘UK tour’ a ranar Alhamis a 1 Mark Lane da ke Landon, lamarin da ya masoyansa ba su ji daɗi ba bayan sun sayi tikitin kallon wasan.
A wani faifan bidiyo ta kafar Instagram jiya Juma’a, an ga 2Face tare da matarsa, inda ya ce bai sami halartar taron ba ne saboda matsalar kiwon lafiya ta gaggawa.
Ya kuma yaba wa masoyan nasa tare da lallashin su, yana mai cewa za a sake shirya wani taron na musamman domin faranta musu.
Mawaƙin mai shekaru 50, a halin yanzu yana Birtaniya da nufin gabatar da wasa a biranen Birmingham, Glasgow, Bristol, Chelmsford, Bournemouth, Sheffield da Cardiff.
A watan Yuli ne 2Baba da Natasha suka yi aurensu cikin sirri, inda tun daga lokacin ake ganin su tare a bainar jama’a.
