Zargin fyaɗe: Ina gida, ba hannun ƴan sanda ba, inji Sanata Abbo

Spread the love

Tsohon Sanatan da ya wakilci mazabar Adamawa ta Arewa, Ishaku Elisha Abbo, ya ƙaryata rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta na cewa ‘yan sanda sun kama shi bisa zargin yin fyaɗe ga wata yarinya ‘yar shekara 13 a Abuja.

A cewar jita-jitar da ta yaɗu a ranar Laraba, an zargi Sanata Abbo da yi wa yarinya ƙarama fyãdæ a gidansa da ke Katampe, Abuja, a ranar 29 ga Yuni, 2025, kuma hakan ya janyo cece-kuce daga jama’a.

Iyalin yarinyar sun kara da cewa Abbo ya yi yunkurin rufe bakin mahaifin yarinyar ta hanyar aika masa da kuɗi, tare da zargin cewa Sanata Aishatu Binani, wacce ta tsaya takarar gwamna a Adamawa a 2023, ta ziyarce su don su janye ƙarar.

Saidai cikin gaggawa, Sanata Abbo ya musanta zargin, yana mai cewa labarin ƙarya ne kuma bai ke hannun ‘yan sanda ba. A wata tattaunawa ta waya da wakilinmu, Abbo ya bayyana cewa har yanzu yana gida cikin koshin lafiya, ba a tsare shi kamar yadda ake yadawa ba.

A cewarsa, zargin wani shiri ne da abokan hamayyar siyasa suka ƙulla domin bata masa suna. Ya bayyana cewa wata mata ce ta nemi kuɗin Naira miliyan 5 daga gare shi, tare da barazanar cewa za ta kai rahoto idan bai biya ba.

Abbo ya ce shi da kansa ne ya kai ƙararsa ga rundunar ‘yan sanda ta FCID, inda aka gayyaci dukkan ɓangarorin domin bincike.

Wannan rikici dai na baya-bayan nan yana cikin jerin matsalolin da suka dabaibaye sanatan tun bayan shigar sa siyasa. A 2019, wani bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta ya nuna shi na dukan wata mace a wani shagon kayan batsa a Abuja, wanda ya jawo masa suka sosai.

Haka kuma, an taɓa zarginsa da yunkurin cin zarafin wata matar aure da wani faifan bidiyon lalata.

Abbo ya kasance Sanata a Majalisar Dokoki ta 9, sannan aka sake zaɓensa zuwa Majalisar ta 10, kafin kotun daukaka ƙara ta soke nasararsa, inda aka maye gurbinsa da Sanata Amos Yohanna.

By Babaji