Majalisar Dokokin Katsina ta yi kira ga gwamnati da ta ƙara yawan jami’an tsaro a Kusada

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Sakamakon sulhu da ‘yan bindiga suka yi da alummomi a ƙananan hukumomin da su kai ta fama da rashin tsaro a jihar a yanzu dai zaman lafiya ya fara samuwa a yankunan.

To sai dai akwai fargaban cewa wasu yan bindiga sun baro waɗannan ƙananan hukumomi zuwa wasu da suke zaune lafiya.

A kan haka ne Majalissar Dakoki ta jihar katsina, tayi kira zuwa ga sashen zartaswa da a ƙara jami’an tsaro a Magama,Sabarawa,Mazoji, Jeri,Duza,Tsohuwarmai Jigira da Kofa dake ƙaramar hukumar Kusada.

A zaman majalisar ɗan majalissa mai wakiltar ƙaramar hukumar Kusada, Hon. Ghali Garba shine ya gabatar da ƙudurin. In da ya roƙi mambobin majalissar da su goya masa, ayi kira zuwa ga majalissar zartaswa domin a ƙara jami’an tsaro a wannan wuraren ƙauyukan domin al’umma su samu kwanciyar hankali daga barazanar ɓarayin daji.

Ƙudurin ya samu cikakken goyan baya daga mambobin majalissar, in da shugaban majalissar Rt. Hon Nasir Yahaya ya bada umarni da a tura wa majalisar zartaswa domin tayi wani abu a kai.

Haka kuma najalisar ta yi dokar da za ta ƙirƙiri hukumar da za ta bunƙasa harkar kasuwanci a Jihar Katsina (Katsina State Trade Facilitation Center), Ƙirƙirar hukumar ya biyo bayan karanta rahoton da shugaban kwamitin da ya jagoranci aikin, Hon. Abduljalal Isma’il ya gabatar a gaban zauren majalissar.

Gwamna Dikko Raɗɗa shine ya turawa majalissar buƙatar ƙirƙirar hukumar domin a bunƙasa harkar kasuwanci a Jihar Katsina, wanda wannan yana cikin ƙudorinsa na bunƙasa harkar kasuwanci a lokacin da yake gudanar da yaƙin neman zaɓe.

By ukarofi