Malam Aliyu Ƙanƙara ya zama farfesa

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Shahararren marubucin Hausa, wanda ya yi fice wajen bincike kan rayuwa da waƙoƙin marigayi Dakta Mamman Shata Katsina, Dakta Aliyu Ibrahim Ƙanƙara ya samu ci gaba a fannin ilimi, inda ya zama Farfesa na farko a fannin ilimin da ya shafi halittun duwatsu (Geology) a Jami’ar Tarayya da ke Dutsin-ma, Jihar Katsina.

Muƙaddashin shugaban jami’ar, Farfesa Aminu Ado ne ya sanar da wannan ci gaba a yayin taron musamman karo na 135 na hukumar zartarwa na jami’ar.

A yayin taron, wanda ya gudana a ɗakin taro na sashin nazarin noma da ke babbar harabar jami’ar, shugaban jami’ar ya bayyana cewa: “Ka sanya mu farin ciki, kuma muna alfahari da kai. Muna fata wannan muƙami zai zama mai amfani ga babbar jami’ar da kuma ƙasa baki ɗaya.”

Wata baiwa da Allah ya ba Farfesa Aliyu Ƙanƙara, ita ce ta rubuce-rubuce a fannin adabin Hausa. Mafi yawan mutane a Arewa, sun fi sanin shi da nazari da rubuce-rubuce a kan rayuwa da waƙoƙin mashahurin mawakin Hausa, marigayi Dakta Mamman Shata Katsina.

Ya rubuta littattafai da maƙaloli da sharhi a kafafen watsa labarai, dangane da abin da ya shafi Shata da waƙoƙin sa.

By ukarofi