
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaba Bola Tinubu ya amince da murabus ɗin Ministan Kimiyya, Ƙirƙira da Fasaha, wato Geoffrey Uche Nnaji.
A wata sanarwa da Kakakin Shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ya fitar a yau Talata, ya ce shugaban ya amince da murabus ɗin Ministan, wanda ya biyo bayan zarginsa da aka yi da amfani da takardar digiri ta bogi.
A ƴan kwanakin nan aka zargi tsohon ministan da yin amfani da digirin bogi daga Jami’ar Nijeriya ta Nsuka, lamarin da ya ja hankalin al’umma, duk da cewa ya musanta.
Njaji ya bayyana cewa, ana masa bita da ƙulli ne, inda ya zargi abokan hamayyarsa a siyasa da yunƙurin ɓata masa suna.
Sanarwar ta ƙara da cewa, Shugaban ƙasar ya yi godiya a gare shi bisa hidimta wa Nijeriya tare da masa fatan alheri.
