Majalisar Dattawa ta amince da ƙwace fasfo na shekara 10 ga ƴan Nijeriyar da aka samu da laifi a ƙasashen waje

Spread the love

Majalisar Dattawa ta amince da haramta wa duk wani ɗan Nijeriyar da aka samu da aikata laifi a ƙasashen waje yin amfani da fasfon ƙasar na tsawon shekaru 10.

Majalisar ta amince da hakan ne yayin zamanta a Abuja, ranar Talata.

Sanata Abubakar Bello mai wakiltar Jihar Neja ta Arewa ya gabatar da ƙudirin ga majalisar a wani ɓangare na yi wa dokar fasfo garambawul.

Ƙudirin ya buƙaci a karɓe fasfo ɗin ne na tsawon shekara 10 mafi ƙaranci, lamarin da ake ganin zai taimaka wajen sanya ƴan ƙasar da ke waje kuma suke aikata manyan laifuka
shiga taitayinsu.

Ƴan majalisar na fatan matakin zai taimaka wajen magance ɓata sunan ƙasar da wasu ke yi a ƙasashen waje.

By Babaji