Al’ummar Gidan Mantau da Mai Farin Kai a Katsina sun karɓi tallafin kuɗi daga hukumar CSDA

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Al’ummar garuruwan Gidan Mantau da Mai Farin Kai na ƙaramar hukumar Malumfashi sun karɓi horo da takardun kuɗi (cheques) daga hukumar inganta rayuwar al’umma ta Jihar Katsina (CSDA), domin gudanar da muhimman ayyukan al’umma da gwamnatin jihar ta yi musu alƙawari.

An gudanar da wannan taro ne a ɗakin taro na sakatariyar ƙaramar hukumar Malumfashi.

A jawabin sa Ko’odinetan shirin KT-CARES na jihar Katsina, Alhaji Nafi’u Muhammad, wanda Alhaji Abdullahi Hudu Ingawa ya wakilta, ya jajanta wa al’ummar garuruwan bisa iftila’in da suka fuskanta sakamakon harin ’yan bindiga.

Ya bayyana cewa manufar shirin KT-CARES ita ce tallafawa al’ummomin da suka shiga cikin irin waɗannan iftala’i domin dawo da rayuwa ta alheri.

Ya kuma yi kira ga shugabannin al’ummomin da suka karɓi amanar gudanar da ayyukan da su tabbatar sun yi amfani da tallafin yadda ya kamata, don amfanin kansu da na al’ummarsu baki ɗaya.

A nasa jawabin, Shugaban hukumar CSDA ta jihar Katsina, Alhaji Muhammad Dikko Abdul’aziz, ya bayyana cewa Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda ne ya bayar da umarnin gudanar da waɗannan ayyuka domin taimakon al’ummar da abin ya shafa.

Ya ce cikin ayyukan da za a gudanar a garuruwan akwai gine-ginen makarantu, asibiti da kuma samar da ruwan sha, kuma dukkan kuɗaɗen da za a yi amfani da su an riga an amince da su.

Alhaji Dikko ya ƙara gode wa Gwamna Radda bisa jajircewarsa wajen taimaka wa al’ummomin da suka fuskanci ƙalubale, yana mai cewa wannan mataki ya nuna irin kulawa da tausayi da gwamnatin jihar ke nunawa jama’a.

Shi ma Shugaban ƙaramar hukumar Malumfashi, Hon. Muntari Abdullahi City, ya bayyana godiyarsa ga Gwamna Raɗɗa bisa wannan shiri na taimako, tare da kira ga al’umma da su yi amfani da damar da aka basu wajen gudanar da ayyuka na gari.

kwanan baya ne yan bindiga suka shiga wani masallaci a garin Mantau yayin da mutane ke gudanar da Sallah inda nan take suka kashe mutane fiye da 50.

A yayin taron, wasu jami’an hukumar sun gabatar da jawabai da ƙasidu kan yadda ake gudanar da ayyukan CSDA. Cikin waɗanda suka gabatar da bayanai akwai Alhaji Magaji Bakori, Malam Ibrahim Dandela, Mas’udu Danladi, Dr. Sama’ila Balarabe, Ahmad Rabi’u Kankia, Aminu Hassan Gafai, Engr. Abbas Sulaiman, Ibrahim Umar da Habiba Abubakar.

Bayan kammala jawabai, an bai wa mahalarta taron damar yin tambayoyi da tattaunawa, kafin daga bisani aka mika musu takardun kuɗin (cheques) na tallafin a bainar jama’a.

By ukarofi