Tanimu ya buƙaci Gwamnatin Gombe ta yi gini don tunawa da Janar Abacha

Spread the love

Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe

Jagoran al’umma kuma jakadan zaman lafiya, kwamared Maishanu Abubakar Tanimu, ya buƙaci Gwamnatin Jihar Gombe da ta karrama marigayi Janar Sani Abacha ta hanyar sanya sunansa a wani muhimmin gini ko babbar hanya, domin tunawa da rawar da ya taka wajen ƙirƙiro da jihar.

Da yake zantawa da wakilinmu a Gombe, Tanimu ya ce al’ummar jihar na da haƙƙin tunawa da Janar Abacha, domin a zamanin sa ne a shekarar 1996 aka kafa Jihar Gombe daga tsohuwar Jihar Bauchi.

Ya bayyana cewa da ba don wannan mataki na tarihi ba, da Gombe ba ta kai matsayin da take a yau ba ta fuskar ci gaban tattalin arziki da gine-gine.

Tanimu ya shawarci gwamnati ta sanya sunan marigayi Janar Abacha a wani babban wuri kamar jami’a, asibitin koyarwa na tarayya ko babbar hanya, a matsayin girmamawa ga wanda ya assasa jihar.

Sannan ya jinjinawa gwarazan da suka yi yaƙin neman jihar irin su Alhaji Adamu Yaro Gombe, da Alhaji Yahaya Umaru da Adamu Ɗan Jarida da suka riga mu gidan gaskiya.

Ya kuma yabawa Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, wanda shi ne shugaban ƙungiyar gwamnonin Arewa maso Gabas, bisa ayyukan raya ƙasa da yake aiwatarwa a faɗin jihar, yana mai cewa gwamnan ya sauya fuskar Gombe ta hanyar “manyan ayyuka” masu tasiri ga rayuwar jama’a.

“Yayin da muke ganin irin ci gaban da ake samu a ƙarƙashin Gwamna Inuwa Yahaya, bai kamata mu manta da waɗanda suka shimfida tubalin wannan cigaba tun farko ba.

Marigayi Janar Sani Abacha ya cancanci a tuna shi da girmamawa,” in ji Tanimu.

Ya buƙaci ‘yan siyasa da al’ummar Gombe gaba ɗaya da su ci gaba da tunawa da irin gudumawar da shugabannin baya suka bayar wajen kafa ta da gina jihar, yana mai cewa, “mu kada mu manta da jarumanmu na baya, domin gudumawarsu ba za ta taɓa tafiya a banza ba.”

By ukarofi