
Rundunar ƴan sanda ta ce ta dakatar da aikin tilasta wa masi ababen bin dokar amfani da gilashi mai duhu ga motocinsu.
Kakannin ƴan sandan Birnin Tarayya Abuja, Josephine Adeh, ta sanar da dakatarwar ga motocin da ke cikin yankin.
Ta bayyana cewa, an ɗauki matakin ne bayan rundunar ta karɓi umarnin kotu daga babbar hedikwatarta da ke Louis Edet House a birnin.
Josephine ta bayyana hakan ne a yayin wata hira da gidan talabijin na AIT a yau Laraba.
Ta kuma ce, umarnin dakatarwar zai cigaba da aiki har sai an kammala shari’ar da ke gudana a kotu.
