Yajin aiki: Tinubu ya yi magiya ga ASUU don guje wa rufe jami’o’i

Spread the love

Gwamnatin Tarayya ta roƙi Ƙungiyar malaman jami’o’i, ASUU da ta janye shirin tafiya yajin aiki, inda ta tabbatar da cewa tana ɗaukar matakai don warware dukkan buƙatun da ƙungiyar ta gabatar.

Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa ya bayyana hakan yayin taron manema labarai a birnin tarayya Abuja yau Laraba.

Ya ce, gwamnati tuni ta fara nazari kan buƙatun ƙungiyar, kuma ana samun cigaba a tattaunawar da ke gudana tsakanin ɓangarorin biyu wajen warware matsalolin.

Ministan ya bayyana cewa an sake kafa tare da kaddamar da Kwamitin faɗaɗa tattaunawa na gwamnatin tarayya kan manyan makarantu karkashin jagorancin Mahmud Yayale Ahmed, domin hanzarta tattaunawa da ƙungiyoyin malaman jami’o’i da na ma’aikatan da ba malamai ba, da kuma na kwalejojin fasaha da ilimi.

Ya ƙara da cewa, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bada umarnin cewa a yi duk mai yiwuwa domin kauce wa sake samun tsaiko a harkokin manyan makarantu.

Wasu rahotanni sun nuna cewa ƙungiyar ta ASUU ta fara shirye-shiryen tura saƙon shirin ko-ta-kwana ga mambobinta domin tsunduma yajin aikin gargadi na ƙasa baki ɗaya na tsawon kwanaki 14 da ta ba gwamnati na daf da ƙarewa.

By Babaji