Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA
Yayin da Nijeriya ta cika shekaru 65 da samun ’yanci daga Turawan ingilishi, an yi jawabai na yabawa gwaraza da su ka jajirce wajen ganin ‘yancin da a ka samu ya amfani al’ummar su. Ai gabanin 1960 a ka shirya ba da ‘yancin, amma hangen nesan Firmiya Sir Ahmadu Bello ya sa a ka jira a shirya don samun al’ummar Arewa su amfana da ribar ’yancin. Da yawa matasan yau ba su san cewa jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria ita ce ta farko a Arewa ba kuma shekaru biyu ne kacal bayan karɓar ’yancin wato a 1962 Gamji ya kaddamar da fara aikin jami’ar. Rashin wadatattun ’yan boko da za su rike madafun iko gabanin samun ‘yancin ya sa Gamji ya ki amincewa da gaggauta karɓar ’yancin sai da a ka tura wasu ’yan Arewa cikin gaggawa su ka yi karatu mai zurfi a ketare su ka dawo. Wannan na daga dalilan da su ka haddasawa Sardauna samun ƙin jini daga wasu kusoshin sashen kudanci musamman kudu maso gabashin Nijeriya. Gamji ya sadaukar da ran sa don Arewa ta amfana. Bawan Allah na da damar arcewa kuma tabbas an ba shi shawara ya fice don hango kisan gilla da ke tafe amma ya ce a’a, ya zauna a nan Kaduna inda nan ne gidan Arewa a yau har miyagun su ka sheƙar da jinin sa amma sam ba su iya rusa ɗimbin alheran da ya shuka ba ciki kuwa har da samar da ’yancin al’ummar Mambilla a jihar Taraba ta yau, su ka zama ‘yan Nijeriya maimakon hade yankin da Jamhuriyar Kamaru.
In ka na karanta tarihi da buɗaɗɗiyar zuciya, za ka iya fahimar Sardauna ya yi amfani da damar da Allah ya ba shi ta jagoranci wajen yin aiyukan alheri ba kakkautawa. Har yau din nan bayan kimanin shekaru 60 da yi wa Gamji kisan gilla, in ka za ga Lardin Arewa na tarihi za ka samu aiyukan Sardauna na nan daram kuma da yawa a na cin moriyar su. Kowane yanki da kowace jiha na da tambarin aikin alheri na Sardauna. Mazan kwarai bai kafa kamfanoni ko gina gidaje don barin gado ga iyalin sa ba, sam-sam amma ya kafa aiyuka da waɗanda ba a haifi iyayen su ko kakannin su a ma lokacin da a ka yi ma sa kisan gilla su ci gajiya. Abun da za mu biya Saraduna shi ne mu wanzar da ayyukan sa na alheri da yi ma sa addu’ar rahamar ubangiji madaukakin Sarki.
Lokacin da na fara ziyartar tsaunin Mambilla bayan mun wuce Baruwa/Sirti mu na magana kan yanda Gamji ya biyo ta wannan hanya tun ba wannan shararrar hanyar mota na san tabbas sadaukar da kai na shugabannin mu da su ka karɓo ‘yanci daga ingilishi ba karamin aiki ba ne da ‘yan ƙalilan ne a yanzu za su iya kamantawa. Da mu ka zo za mu fara hawa wannan dogon tsauni an ba ni tarihi cewa an buƙaci Sir Ahmadu Bello ya tsaya a nan ba sai ya hau sama ba inda wani ya yi Sakkwatanci don ruwaito abun da Gamji ya gwada ya na cewa “tun da akwai jama’ar mu kan tsaunin ga hawa mu kai” Nan Amadu ya jagoranci tawaga wajen hawa tsaunin da har dai mota ta sullubo wajen haurawa sai nisan kwana ka iya tserar da mutum daga rasa rai. Ko a yau in mutum bai san hanya ba akwai waɗanda a ke kira ‘yan dutse da za su karɓi dan mabudin mota su haurar da mutum ya biya ladar aikin su. Kama daga garin Mai-Samari, Gurgu zuwa can tsakiyar Garin Nguroje, Mayo Ndaga, Kakara mai ganyen shayin HIGHLAND ko can babban birnin ƙaramar hukuma Gembu haziƙar kafar Firimiya ta taka. Burin Amadu ya tabbatar da zaman lafiyar jama’a da samun cin moriyar ayyukan gwamnati.
Hakika duk wanda ya samu damar haurawa kan tsaunin nan zai tabbatar tamkar ba a nan Nijeriya ya ke ba kuma don wahalar tafiya tsaunin, mazauna can sun fi hulɗar da garuruwan Jamhuriyar Kamaru da ke makwabtaka. Gamji ya dau matakan wayar da kan al’ummar Mambilla su rungumi harkokin ilimi da kaucewa bambance-bambance. Yankin ya cigaba da riƙe sunan sa na Mambilla amma sai ma bayan shekaru 10 da yi wa Gamji kisan gilla da mashaya jini su ka yi kantoman mulkin soja na tsohuwar jihar Gongola Manjo Janar Muhammad Jega ya radawa Mambilla sunan Sardauna “ƙaramar hukumar Sardauna” don karrama gudunmawar da Gamji ya bayar da ta tabbatar da mika yankin ga Nijeriya maimakon Jamhuriyar Kamaru.
Duk wanda ya zama mai adalci kuma ya nazarci irin arzikin da Allah ya shunfada a yankin Mambilla Filato na noma da kiwo don kyakkyawan yanayi na sanyi da albarkar kasa, zai yi wa Firimiya Ahmadu Bello addua’r rahama. Hangen nesan wannan barden jagora ya zama abun yabo da buƙatar waɗanda Allah ya ke ba wa dama su hau madafun iko a yau su yi iya bakin ƙoƙari wajen koyi da Sardauna. Shugabancin Sardauna na zama tamkar ka dasa bishiya da za ta girma ta ba da inuwa ga jama’a ko bayan ran ka. Ko jama’ar sun sani ko sun butulce in sun sha inuwar bishiyar za ka samu lada. Alheri gadon barci. Shin da me ka ke tuna Gamji mazan kwarai? Ga nan aiyukan sa na alheri birjik sai wanda ka zaba. Na yi nazari na fahimci duk ma wasu abubuwa da mu ke tinƙaho da su a Arewa na nunawa baki, Gamji ne ya assasa su. NDA Kaduna, ABU Zaria, NDDC, Rediyon Nijeriya Kaduna, Cibiyar nazarin noma ta ɓom a Filato da sauran su da daman gaske.
Abun mamaki ina zagawa a Gembu a na nuna min gidajen wasu manyan mutane ciki da waɗanda su ka rike madafun iko a matakin taraiya amma har na gaji ban ji an ce min ga gidan Sardauna ba! Amadu bai yi mulki don tara dukiya ba kuma bai arce don tsoron bakin bindiga ya bar al’ummar sa ba. Garin Gembu mai ban sha’awa na zama wani yanki na yawon buɗe ido inda mutane daga ciki da wajen Nijeriya ke kai ziyara don cin moriyar yanayin da bai gurbata da hayakin masana’antu ba. A yayin da Amadu ya haura tsaunin nan ta kasa, wasu da su ka zo a baya ba sa iya yin hakan sai da taimakon jirgi mai saukar angulu kuma in sun isa Gembu su na da manyan gidajen su na shaƙatawa. Ina amfanin tara abun duniya mutum ya bar baya da kura. Shi ya sa irin su Gamji ba wannan ne damuwar su ba sam, ba barin tarin kuɗi ko gidaje ba amma barin tarin aiyukan alheri da na baya za su ci moriya kuma in sun yi tunani su yi addu’ar alheri. Na nanata duk wanda ka ga ya aibanta Gamji to kar ka raba daya biyu ko dan kwangilar rusa Arewa ne daga ɗaukar nauyin makiya, ko yaro dan bana bakwai da bai san inda duniya ta sa gaba ba. Har ila yau ina sake amfani da wannan dama wajen kira ga matasa maza da mata a farka don watsi da mummunan kamfen ɗin rura wutar ƙabilanci a yankin Arewa mai albarka.
KAMMALAWA
Ayyukan da Gamji ya dasa a Arewa na alheri na da wuyar ƙidayuwa don sai ka na rubuta wannan sai wani ya tuna ma ka ai ga wancan ma. Damuwa ta ɗaya ita ce ‘yan bokon da su ka amfana da samun karatu kyauta albarkacin ayyukan Sardauna na karewa don ajali da ke kan kowa kuma ba a samun magadan su da himmar kamantawa. Haƙiƙa wasu daga cikin waɗanda su ka ci gajiyar alherin Gamji sun dasa daga inda ya tsaya. Maimakon a zamanin yau mu ga matasa na tashi da dattijantaka da ƙaunar Arewa sai da yawa daga cikin su, su ka ɗau ɗabi’ar aron al’adun Turawa ko na wasu jama’ar ƙetare hatta daga yadda su ke sanya kaya. A yau za ka ga matashi da aski kamar na zanen dujjal. Mata su kara gashi kamar tozon rakumi. Sana’ar rawa da waka ta hanyar batsa da fitsara sun zama abun ya yi. Badala da yaɗa ɓarna a na gani ita ce hanyar neman kuɗi. Sakarci da koyi da ‘yan daudu na zama abun burgewa. Yaro karami da bai daɗe da fara saka dogon wando ba zai kalli dattijo ya zunduma ma sa ashar da sunan sabuwar duniya sabon ya yi. Na ga wani dattijo a wata kafa ya yi magana ta jan hankali ga wasu matasa da su ka fitsare kafar su, nan take su ka shiga aibanta shi da ma zagin sa. Wannan dattijon fa na daga wadanda su ka yi suna wajen kare muradun Arewa amma don yanda matasan nan su ka yi nisa da shakar iskar duniya ba su raga ma sa ba. Hanya daya da ta rage ita ce ni da kai da mu ke ganin a na yi ba daidai ba, mu gyara aƙalla mutanen da su ke karkashin mu don za su iya sauraron mu. Kazalika sai mu bi da addu’a don ba abun da ya gagari Allah. Yayin da mu ke addu’ar kuma mu riƙa haɗawa da neman gafarar ubangiji don samun yafiyar laifukan da mu ka yi da sani ko bisa kuskure.
