Lakurawa sun kashe ’yan sanda biyu a Natsini da ke Kebbi

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Kebbi 

Da yammamacin ranar Larabar da ta gabata ne waɗansu mahara da ake kyautata zaton ’yan ta’addar Lakurawa ne a kan babura 10 ɗauke da miyagun bindigogi suka kai farmaki a ƙauyen Natsini mai nisan kimanin kilomita 10 daga garin Argungu a Jihar Kebbi, inda suka kashe ‘yan sanda biyu da ke bakin aiki a kan babbar hanyar da ta haɗa Nijeriya da Jamhuriyar Nijar.

Wani mazaunin garin Natsini da bai so a bayyana sunan sa ba ya bayyana cewa ya shi da idon sa ya gan su a lokacin da ya ke kan hanyar sa ta zuwa Bachaka inda suka zo wani gidan mai da ke kusa da mahadar zuwa Augie.

Shigar su gidan man ke da wuya sai kowa ya gudu har da ‘yan sandan da ke bakin aiki kusa da gidan man sai babura biyu daga cikin Lakurawan suka bi su kan babura suka harbe ‘yan sanda biyu da shiga jeji yayin da sauran suka gudu cikin mota.

Ya kuma ƙara da cewa waɗannan mutanen da alamu dai Lakurawa ne saboda ya gan su kusa-kusa da shi kuma duk da yake waɗansu daga cikinsu sun rufe fuskokinsu amma dai ana iya ganin kitson gashin kawunansu.

Wata majiya daga ƙauyen ta tabbatar da cewa waɗannan Lakurawan dai ba su shiga garin ba sai dai bayan da suka cika baburansu da mai suka juya suka koma ta hanyar Bachaka da ke kan iyakar Nijeriya da Jamhuriyar Nijar.

Wakilin Blueprint Manhaja ya yi ƙoƙarin jin ta bakin rundunar ‘yan sandan Kebbi ta hanyar jami’in hulɗa da jama’a Sufurtanda Nafi’u Abubakar sai dai hakan ba ta samu ba kuma har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton ba wata sanarwa daga rundunar.

Sai dai wani jami’in tsaro ya bayyana cewa tun ranar laraba da abin ya faru ba a sami dauko gawarwakin jami’an ‘yan sandan ba sai zuwa ranar Alhamis inda bayan an gano gawarwakin aka ɗauke su zuwa asibiti.

Ya kuma ƙara da cewa jami’an ‘yan sandan suna aiki ne a ƙarƙashin ‘yan sandan manyan hanyoyi ne da ka fi sani da High way patrol.

By ukarofi