Ana ci gaba da jimamin rasuwar fitaccen ɗan jarida, Alhaji Sulaiman Bala a Kaduna

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Jama’a a faɗin Jihar Kaduna da ma wasu sassan Arewa da Nijeriya baki-ɗaya suna ci gaba da nuna jimami kan rasuwar fitaccen ɗan jarida kuma dattijo mai kishin al’umma, Alhaji Sulaiman Bala, wanda Allah ya yi wa rasuwa a daren ranar Lahadi da ta gabata, 5 ga Oktoba, 2025.

Alhaji Sulaiman Bala ya rasu yana da shekaru 71 a duniya, inda ya bar mata huɗu da ’ya’ya 35 — mata 15, maza 20. Ya rasu bayan ya yi fama da gajeriyar jinya, kafin Allah Ya karɓi rayuwarsa.

Marigayin ya shahara wajen bayar da gudunmawa ga harkar jarida a Jihar Kaduna da ma ƙasa baki-ɗaya.

Ya kasance ɗaya daga cikin tubalan farko da suka share wa matasa fagen aikin jarida a Arewa, inda ya ke bayar da shawara, tallafi da ƙarfafa gwiwa’yan jarida masu tasowa.

Wasu daga cikin ’yan jarida da Blueprint Manhaja ta zanta da su sun bayyana shi a matsayin “bango da ginshiƙi” a wannan fanni. Dillalan jaridu sun bayyana cewa, marigayin mutum ne mai gaskiya, himma da taimakon al’umma.

Marigayin ya kasance mahaifi ne ga fitaccen ɗan jarida kuma Kakakin Gwamnan Jihar Zamfara, Idris Sulaiman Bala, wanda ya shahara wajen gudanar da aikinsa cikin ƙwarewa, gaskiya, natsuwa da jajircewa — halaye da ake ganin ya gada daga mahaifinsa.

Bugu da ƙari, Alhaji Sulaiman Bala yana daga cikin ’yan uwa Musulmi masu ƙoƙari, waɗanda suka shafe shekaru suna hidima ga addinin Musulunci, musamman wajen taimakon marayu, gajiyayyu da talakawa.

Sheikh Malam Isa Badarawa ya bayyana marigayin a matsayin mutum mai kirki, hangen nesa da tunani mai zurfi, wanda kullum ya ke son ganin al’amura suna tafiya bisa tsari.

Maƙwabtansa sun bayyana shi a matsayin mutum mai sauƙin kai, tausayi da karamci, wanda ya kasance abin koyi ga kowa.

Sun yi addu’ar Allah Ya jiƙan sa, ya gafarta masa, ya kuma sanya shi cikin rahamarsa.

Lallai Alhaji Sulaiman Bala ya bar babban giɓi a zuciyar al’umma da makusanta mai wuyar cikewa, domin mutum ne da aka sani kan roƙo da mai gaskiya, adalci da ƙishi na cigaban ƙasa.

By ukarofi