A tsawon shekaru, tattalin arzikin Nijeriya ya sha fuskantar ƙalubale iri-iri – daga hauhawar farashi, sauyin farashin mai, zuwa raguwar darajar Naira. Amma a halin yanzu, ana ganin wasu sabbin alamun farfaɗowa da haɓaka, abin da ke nuna cewa ƙoƙarin Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya fara haifar da sakamako mai kyau.
Bisa bayanan da hukumomin gwamnati suka fitar, an samu ci gaba a GDP na ƙasa da kashi 4.4%, tare da ƙaruwa a ajiyar kuɗaɗen ƙasashen waje zuwa dala biliyan 42. Wannan kuwa ba ƙaramin ci gaba ba ne, musamman idan aka yi la’akari da rikicin tattalin arzikin duniya da ya taso daga hauhawar farashin mai da tasirin yaƙin Ukraine da Rasha.
Shugaba Tinubu ya sha nanata cewa manufarsa ita ce ta “Renewed Hope Agenda”, wadda ke nufin dawo da amincewar jama’a cikin tsarin tattalin arziki mai zaman kansa. A ƙarƙashin wannan shiri, gwamnati ta ɗauki matakai da dama – ciki har da rage tallafin mai, daidaita musayar kuɗi, da kuma inganta yanayin kasuwanci domin jawo hannun jari daga waje.
Ko da yake waɗannan matakai sun kawo wuya a farko, musamman ga talakawa, akwai alamun cewa sun fara haifar da sakamako mai kyau. Masana sun lura da cewa kasuwannin hannayen jari sun fara nuna ƙarfi, kamfanoni masu zaman kansu sun fara fitar da sababbin ayyuka, kuma hukumomin kuɗi na duniya kamar IMF da Bankin Duniya sun fara nuna amincewa da dabarun gwamnatin Nijeriya.
A gaskiya, abin da ake buƙata yanzu shi ne ci gaban daidaito tsakanin manufofi da aikace-aikace. Gwamnati ta riga ta kafa ginshiƙai, amma akwai buƙatar tabbatar da cewa ribar tattalin arziki ta sauka har ƙasa – wato ta shiga hannun talaka. Wannan na nufin ƙarin ayykan yi ga matasa, da kuma tallafi ga masana’antun cikin gida domin rage dogaro da kaya daga waje.
Haka kuma, akwai buƙatar gwamnati ta ci gaba da inganta bayanai da gaskiya a cikin manufofin kuɗi da kasafi, domin tabbatar da cewa jama’a suna ganin amfanin gyaran da ake yi. Idan aka ci gaba da wannan tafiya, Nijeriya za ta iya komawa kan turbar da aka daɗe ana jira.
Haɓakar tattalin arziki ba ta samuwa cikin dare ɗaya. Amma matakin farko shi ne ƙwarin gwiwa da hangen nesa, wanda gwamnatin Tinubu ta nuna. Idan aka ci gaba da tafiya cikin gaskiya da tsari, akwai yiwuwar cewa Nijeriya za ta shiga sabon babi na tattalin arzikin gaskiya da ɗorewa.
