An karrama Abdulkareem Mohammed na KILAF a bajekolin fim a Kaduna

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Alhaji Abdulkareem Mohammed, wanda shi ne ya kafa ƙungiyar kasuwancin fina-finan Kano (KILAF), ya samu kyuatar karramci a babban taron ƴan fim na ƙasa-da-ƙasa da aka gudanar a Jihar Kaduna.

A safiyar yau Dakta Ahmed Sarari ya gabatar wa Shugaban na KILAF kyautar a Jihar Kano.

Abdulkareem Mohammed shi ne darakta manaja na Kamfanin Moving Image Limited, wanda ɗaya ne daga cikin kamfanonin harkokin fina-finai a jihar ta Kano.

Haka kuma yana ɗaya daga cikin waɗanda suka samar da Ƙungiyar Ƴan Fim ta Ƙasa (MOPPAN).

Ya bada gagarumar gudumawa a masana’antar fina-finai musamman a yankin arewacin Nijeriya.

By Babaji