‘Yan sanda sun cika hannu da waɗanda ake zargi da kisan ƴar jaridar Arise News, Sommie Maduagwu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Rundunar ƴan sanda a Abuja, ta yi nasarar kama ƴan fashin da ake zargi da kisan ƴar jaridar gidan talabijin na Arise News, wato Somtochukwu Christella Maduagwu da wani mai gadi.

Mamatan sun rasu ne sakamakon wani fashi da aka ƙaddamar a rukunin gidaje na Unique Apartment da ke Ƙauyen Gishiri a Gundumar Katampe da ke birnin tarayyar.

Al’amarin ya auku ne a ranar 29 ga watan Satumba, 2025, a lokacin da wasu ƴan fashi suka farmaki al’umma a yankin, inda suka halaka mutanen biyu da tserewa da wasu kayayyaki masu daraja.

Rahotanni sun bayyana cewa, Sommie ta rasu ne a lokacin da ta dirƙo daga gidan da take mai hawa uku da nufin tserewa, lamarin da ya sa ta samu munanan raunuka.

Shi kuwa mai gadin ya rasu ne a lokacin da ya yi taho mu gama da ɓarayin.

Da take tabbatar da kamen a jiya Alhamis, rundunar ta ce an kama kimanin mutane 12 da ake zargi da hannu a faruwar al’amarin bayan wani atisaye da tawagar kunama ta ‘Scorpion Squad’ ƙarƙashin jagorancin ACP Victor Godfrey ta gudanar da haɗin-gwiwar jami’an sashen bayanan sirri.

Waɗanda aka kama akwai sune:
Shamsudeen Hassan daga Malumfashi a jihar Katsina; Hassan Isah mai shekaru 22 daga Zaria a jihar Kaduna; sai Sumayya Mohammed (a.k.a. Baby) mai shekaru 27 daga Saminaka a Kaduna.

Sauran sun haɗa da; Isah Abdulrahman (a.k.a. Abbati) mai shekaru 25 daga Zaria; da kuma Musa Umar (a.k.a. Small) ɗan shekara 31 daga Maiduguri a Borno.

Rundunar ta ƙara da cewa, an yi nasarar kama su ne sakamakon bin diddigin wayoyin salula da aka sace a yayin fashin.

By Babaji