Shugaban ƙaramar hukuma ya halarci bikin auren ‘ya’yan ‘yan bindiga a Katsina

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaban Ƙaramar Hukumar Sabuwa a Jihar Katsina, Injiniya Sagir Tanimu ya halarci ɗaurin auren ƴaƴan wasu ƴan bindiga bayan sulhu da su a jihar.

Hakan na zuwa ne makonni kaɗan da aka yi sulhu tsananin gwamnatin da ƴan bindigar da ke ayyukansu a yankin, kamar yadda Sahara Reporters ta ruwaito.

Waɗanda suka mara wa shugaban Karamar Hukumar baya sun haɗa da Wakilin Masarauta, Alhaji Ibrahim Bello Kogo, Yariman Sarkin Kogon Katsina da kuma Hakimin Sabuwa.

Hakan na da nufin cewa zaman lafiya ya fara dawo wa wasu yankunan jihar Katsina.

To amma duk da haka mazauna sun yi gargaɗin cewa sulhu na gaskiya zai samu ne a yayin da ƴan bindigar suka janye kai hare-hare da ajiye makamansu baki ɗaya.

A kwanakin baya ne jami’an gwamnatin Katsina da wasu sarakunan gargajiya a jihar suka ƙaddamar da taron sulhu da ƴan bindiga a Karrama Hukumar Matazu da ke jihar.

Haka ma a Ƙaramar Hukumar Faskari duk a jihar, inda nan ma an samu gudanar da zaman sulhu da ƴan bindigar yankin.

Hukumomi sun shaida cewa, sulhu da ake yi da nufin daƙile ayyukan rashin tsaro a jihar yana fuskantar ƙalubalen sake kai waɗansu hare-hare da garkuwa da mutane daga baya.

By Babaji