An naɗa Farfesa Uduma Uduma a matsayin VC na Jami’ar NOUN

Spread the love

Jami’ar National Open University of Nigeria a Abuja (NOUN), ta sanar da naɗa Farfesa Uduma Uduma a matsayin sabon Shugaban Jami’ar (VC).

Shugaban Kwamitin Gudanarwar Jami’ar, Malam Isa Yuguda ya bayyana hakan yayin taron manema labarai ranar Juma’a a birnin tarayya Abuja.

A cewar Yuguda, Farfesa Uduma zai karɓi ragamar shugabancin jami’ar daga hannun Farfesa Olufemi Peters, wanda wa’adinsa zai ƙare a watan Fabrairu 2026.

Nadin ya biyo bayan shawarwarin da Kwamitin Haɗin Gwiwa na Majalisar Gudanarwa da Majalisar Malamai suka bayar, wanda majalisar ta yi nazari a kai kana daga bisani ta amince.

A ranar 30 ga watan Janairu, 1966 aka haifi Farfesa Uduma, wanda ya kammala digirinsa na farko a Jami’ar Kalaba a matsayin ɗalibin da ya fi kowa ƙwazo a tsangayarsa.

Daga bisani ya zama dakta a fannin Nazarin Halayyar Ɗan-adam a Jami’ar Lagas. A shekarar 2007 ne kuma ya zama lauya.

By Babaji