
Ministan Albarkatun Ƙasa, Dele Alake ya ce ya ninka yawan jami’an da ke tsaron sa sau uku sakamakon samun barazanar kisa daga wasu mutane da kamfanoni da aka soke musu lasisin haƙar ma’adinai saboda ƙin bin dokokin da gwamnati ta shimfiɗa musu.
Ya ce, barazanar ta fito ne daga waɗanda suka yi fushi da yadda ma’aikatarsa ke aiwatar da dokokin da aka jima ana watsi da su.
Ministan ya bayyana hakan ne a taron manema labarai a Abuja gabanin taron satin masu haƙar ma’adinai na ‘Nigeria Mining Week’ wanda zai gudana daga 13 zuwa 15 ga Oktoba, 2025.
Ya bayyana ce wasu daga cikin masu lasisin da aka soke suna amfani da barazana da yaudara ta kafafen yaɗa labarai domin hana gwamnati cigaba da ayyukanta na gyare-gyare a sashen ma’adinai.
“Na karɓi saƙonni da dama na barazanar kisa, amma ba zan ja da baya ba. Mun ɗauki matakin ƙara tsaro domin kare kai daga waɗanda ke jin an tauye musu haƙƙi”, inji Ministan.
Rahotanni sun nuna cewa barazanar ta biyo bayan soke lasisin hakar ma’adinai sama da 3,700 da ma’aikatar ta yi cikin shekaru biyu da suka wuce. Saidai hakan ya saba wa umarnin Shugaba Bola Tinubu na taƙaice yawan jami’an tsaron ministoci zuwa guda biyar kacal.
Kazalika, ya ce gwamnati za ta cigaba da aiwatar da dokoki don tabbatar da gaskiya da tsari a ɓangaren ma’adinai – “waɗanda suka samu lasisi shekaru goma ba tare da biyan kuɗin sabis ko fara aiki ba, dole ne su rasa haƙƙinsu.”
Ya kuma gargadi kamfanonin da ke son kai ƙara ƙasashen waje, inda ya ce babu wani alkali da zai goyi bayan masu karya doka da nufin yi wa ƙasa zagon-ƙasa.
