Sufeto Janar ya rufe sansanin Amotekun kan zargin kashe-kashe da tatsar kuɗaɗe a ƙauyen Osun

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

An samu sabbin bayanai game da abinda ya sa Sufeto Janar na ƴan sanda ya umarci a rufe sansanin jami’an Amotekun na Jihar Osun da ofishinsu na Ife ta Tsakiya bayan zargin su da hannu a wani hari da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama da raunata wasu a Ƙauyen Akinlalu da ke Ƙaramar Hukumar Ife ta Arewa.

Rahotanni sun bayyana cewa, Sufeton ya ɗauki matakin ne sakamakon kisan mutane uku ƴan gida ɗaya da wani mutum ɗaya a lokacin da jami’an suka kutsa kasuwar Akinlalu a makon da ya gabata.

Haka kuma wasu da dama sun jikkata sakamakon harbe-harben bindigogi a yayin atisayen jami’an.

Bayan haka ne Kwamandan Amotekun na Osun, Isaac Omoyele ya yi ikirarin arce wa farmakin kisa, zancen da masu binciken ƴan sanda suka ƙaryata da bayyana shi a matsayin abin ruɗarwa.

Jami’an atisayen sirri (IRT) na rundunar ƙarƙashin umarnin Sufeton, sun yi nasarar kama jami’an Amotekun guda 25 ya daren ranar Laraba wayewar Alhamis.

Sannan, sun rufe sansanin makamansu na Oke-Fia da ke Osogbo da ofishinsu na Ife ta Tsakiya, waɗanda za su cigaba da zama a haka har zuwa lokacin kammala bincike.

Hallau, a yayin bincikensu jami’an na IRT sun gano wasu ɗakunan rufe masu laifi da ke da sashe ta ƙarƙashin ƙasa da Amotekun ke amfani da su wajen kulle waɗanda ake zargi da laifi ba bisa ƙa’ida ba.

By Babaji