Majalisar Wakilai na yunƙurin ganin an sanya ido kan Kirifto

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Majalisar wakilan Nijeriya ta fara yunƙurin ganin an ɗauki matakan sanya ido kan harkokin da suka shafi hada-hadar kuɗaɗe na intanet na kirifto da na’urar POS.

A ranar Litinin ne kakakin majalisar, Abbas Tajudeen ya ƙaddamar da wani kwamiti wanda zai duba amfani ta ɓangaren tattalin arziki da yadda za a sanya ido kan su da kuma tsaron hada-hadar da ake yi ta hanyar intanet.

A jawabin da ya gabatar kakakin majalisar ya ce matakin ya zama dole, idan aka yi la’akari da damuwar da ake nunawa kan damfara da manyan laifukan intanet da samar da kuɗaɗen don aikata ta’addanci da ayyukan masu kirifto da na POS da ke cutar da masu mu’amala da su.

Inda ya ƙara da cewa, rashin dokoki na zahiri da sauye-sauye da sarƙaƙiyar da ke tattare da fasaha, suka sa dole majalisar ta kafa wasu dokoki na sa ido da kula, da kuma bayar da kariya ga masu amfani da kirifto da kuma POS a ƙasar.

Ana sa ran kwamitin zai yi zaman jin bahasi don tattara bayanai daga masu ruwa da tsaki domin taimaka wa majalisar wajen yin dokar da zata tsara yadda za a tafiyar da ayyukan kirifto da sauran ayyukan hada-hadar kuɗaɗe na intanet a ƙasar.

By ukarofi