Gwamnatin Katsina ta ƙulla yarjejeniya da wata ƙungiya da ke ƙasar Belgium kan cutar kansa

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamnatin Jihar Katsina ta sanya hannu kan yarjejeniya da wata kungiya mai suna Revive daga ƙasar Belgium domin tallafa wa mata wajen gano da kuma maganin cututtukan kansar ciwon nono da na mahaifa.

A ƙarƙashin wannan haɗin gwiwa, likitoci 25 daga Belgium za su zo Katsina domin bayar da kulawar lafiya, gudanar da gwaje-gwaje, tare da horas da ma’aikatan lafiya na cikin gida har na tsawon mako biyu.

Kwamishinan Lafiya, Hon. Musa Adamu Funtua, ya bayyana wannan yarjejeniya na nufin ƙara ƙaimi wajen yaƙi da cutar kansa a tsakanin mata a jihar.

Uwargidan Gwamna, Hajiya Fatima Dikko Raɗɗa, ta bayyana farin cikinta da wannan mataki, tana mai cewa zai kawo sauyi wajen samar da kulawar lafiya mai inganci ga mata.

Ita kuwa Kwamishinar Harkokin Mata, Hajiya Hadiza Yar’adua, ta bayyana cewa likitoci uku daga Katsina za su je Belgium domin samun ƙarin horo a asibiti na ƙasar.

Wannan haɗin gwiwa zai taimaka wajen ƙarfafa fannin kiwon lafiya, musamman wajen magance cututtukan da ke addabar mata a Jihar Katsina.

By ukarofi