Daga JAMIL GULMA a Birnin Kebbi
Gwamnan Jihar Kebbi Malam Nasir Idris ya umarci hukumar makarantar kimiyar lafiya da ke Jega da ta kira ɗaliban da aka kora sanadiyyar wani zanga-zangar da suka yi wa tsohon shugaban makarantar Alhaji Sa’adu Haruna Sauwa a shekarar 2024 wanda ya yi sanadiyyar rufe makarantar.
Sanarwar ta fito ne daga bakin shugaban makarantar Malam Hussaini Aliyu yayin wata ganawa da manoma labarai ranar Juma’ar da ta gabata.
Shugaban makarantar ya bayyana cewa yanzu haka dai mai girma gwamna Malam Nasir Idris ya ware naira miliyan sittin (₦60m) don ɗaga darajar waɗansu kwasa-kwasai takwas a sashen kimiyya da hukumar ilmin kimiyya ta yi wanda rashin aiwatar da shi ne a makarantar silar zanga-zangar.
Ya kuma ƙara da cewa duk ɗaliban da aka kora ranar 17 ga watan Oktobar shekarar 2024 za a kira su su dawo su cigaba da karatu da zarar an kammala shirye-shiren.
Ya ce tuni gwamna ya bayar da aikin gyaran ɗakunan kwanan ɗaliban wanda yana daga cikin shirye-shiren mayar da ɗaliban don samun yanayin karatu mai tsafta.
Ya kuma bayyana cewa bayan kammala ɗaga darajar kwasa-kwasan aƙalla ɗalibai 250 ne ake sa ran za su sami takardar shaidar diploma ta ƙasa (National Diploma) a maimakon diploma mai ƙaramar diploma (Ordinary Diploma) wanda shi ma yana daga cikin abubuwan da suka ruruta wutar zanga-zangar.
