Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Gwamnatin Jihar Kano ta amince da Naira biliyan 1.6 domin tallafawa shirin auren zawarawa da ‘yan mata masu niyyar yin aure.
Kwamishina yaɗa labarai da harkokin cikin gida, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ne ya tabbatar wa da Mataimakin Darakta na hukumar hisbah ta Jihar Kano, Sheikh Mujahid Aminudeen, ya bayyana cewa: “Muna shirin gudanar da auren zawarawa ga wani rukuni mai ɗauke da ma’aurata 2,000, kamar yadda gwamnatin jihar ta umarta.”
Ya ƙara da cewa dukkan ma’auratan da suka yi rajista dole ne su je a duba lafiyarsu ta jiki domin tabbatar da halin lafiyarsu, ciki har da cututtukan HIV/AIDS, Hepatitis, jini (genotype), da kuma gwajin amfani da miyagun ƙwayoyi, da sauransu.
“Duban lafiya na cikin muhimman sharuɗɗan shirin auren, wajibi ne, domin duk wanda bai je a duba lafiyarsa ba, za a cire shi daga cikin waɗanda za su ci gajiyar shirin nan take,” in ji shi.
Ko a shekarar 2023, gwamnatin jihar Kano ta ɗauki nauyin auren ma’aurata 1,800, wanda ya ƙunshi maza da mata 3,600 gaba ɗaya.
