Sojoji sun buƙaci haɗin gwiwa da kafafen yaɗa labarai don yaƙi da labaran ƙarya da AI

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Babban Hafsan Sojan ƙasa na Nijeriya (COAS), Laftanar Janar Olufemi Oluyede, ya yi kira da a ƙarfafa haɗin kai tsakanin sojoji da kafafen yaɗa labarai, domin fuskantar barazanar da ta taso daga yaɗa labaran ƙarya da fasahar ƙirƙirarriyar basira ta AI.

Janar Oluyede ya yi wannan kiran ne a ranar Talata yayin buɗe taron horar da manema labarai na sashen hulzar jama’a na rundunar sojan ƙasa na watanni na uku da na huɗu, wanda aka gudanar a Cibiyar Albarkatun Sojan Nijeriya (NARC) da ke Abuja.

Ya samu wakilcin Kwamandan Sashen Yaƙin Yanar Gizo na Sojan Nijeriya, Manjo Janar Mohammed Tanimu Abdullahi, inda ya jaddada cewa jarida mai ɗaukar nauyin gaskiya ta zama muhimmin ginshiƙi kamar dabarun soja wajen kare tsaron ƙasa.

“A yau nasara ba a filin daga kawai ake samun ta ba. Yanzu ana fafatawa ne a fagen bayanai — inda labarai, ra’ayoyi da amincin jama’a ke zama makaman yaƙi,” inji shi.

Hafsan sojan ya yi gargaɗi cewa yawaitar ƙirƙirar abubuwa na ‘deepfake’, labaran ƙarya, da hotunan da aka gyara ta dijital — musamman da taimakon AI — na lalata amincin jama’a da tasirin ayyukan tsaro.

“Labaran ƙarya da hotunan da aka canja na zama barazana ga haɗin kan ƙasa.

Aikinmu shi ne mu tabbatar da cewa gaskiya da bayanai masu tabbas su fi rinjaye a cikin tattaunawar jama’a,” inji Oluyede.

Ya kuma bayyana muhimmancin rawar da kafafen yaɗa labarai ke takawa wajen gina fahimtar jama’a kan sojoji, inda ya roƙi ’yan jarida su kiyaye ƙa’idojin aikin su kuma tabbatar da rahotanni masu daidaito da amfanar ƙasa.

“Kafafen yaɗa labarai abokan hulɗa ne masu muhimmanci wajen gina fahimtar jama’a, samun goyon baya, da kuma nuna sadaukarwar dakarunmu,” inji Janar Oluyede.

Ya ce, taron horon yana cikin ƙoƙarin rundunar sojan ƙasa na ƙara inganta sashen hulɗar jama’a da ƙarfafa dangantaka tsakanin sojoji da farar hula.

Hafsan ya kuma yaba wa Laftanar Janar Appolonia Anele, wadda ke riƙon muƙamin Daraktar Hulɗar Jama’a ta Sojan ƙasa, saboda jajircewarta da ƙoƙarinta na ƙarfafa hulɗar soja da kafafen labarai.

A nata jawabin, Appolonia Anele ta jaddada muhimmancin haɗin kai tsakanin soja da kafafen yaɗa labarai a cikin sabon tsarin tsaron ƙasa da ke ƙara rikitarwa.

Ta yi gargaɗi cewa yaɗa bayanan ƙarya ta AI da sarrafa hotuna ta fasaha na zama babbar barazana ga tsaron ƙasa, don haka ta buƙaci kafafen labarai su kasance masu faɗakarwa da ɗa’a.

Game da taken taron, “ƙara fahimtar jarida mai ɗaukar alhakin rahoto kan ayyukan Sojan Nijeriya a cikin yanayin haɗin gwiwar hukumomi don ƙarfafa tsaron ƙasa,” Anele ta ce manufar ita ce ƙarfafa ilimin aikin jarida na gaskiya a zamani da ake amfani da fasahohin dijital wajen yaɗa bayanan ƙarya da ƙirƙirar hotuna.

“Kafafen yaɗa labarai ba masu kallo ba ne kawai, abokan haɗin gwiwa ne a aikin kare ƙasa,” inji ta.

Ta bayyana taron a matsayin mataki mai muhimmanci wajen ƙarfafa haɗin kai tsakanin sojoji da kafafen yaɗa labarai a yaƙin da ake yi da rashin tsaro, musamman ganin yadda makiyan ƙasa ke amfani da AI da kafafen sada zumunta wajen yaɗa ƙarya da rage wa dakarun ƙwazo.

“A yau, yakin ba da bindiga kawai ake yi da shi ba, ana yin sa ne a fagen bayanai,” inji ta.

Anele ta ƙara da cewa taron yana da alaƙa kai tsaye da manufar hafsan sojan ƙasa na gina runduna mai ƙwarewa, mai ƙwazo, wadda za ta iya aiki cikin haɗin gwiwar hukumomi daban-daban.

By ukarofi