Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Shugaban gungun kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya ƙaddamar da aikin ginin masana’antar takin zamani a birnin Gode da ke yankin Kudu maso Gabashin Habasha.
Masana’antar, wacce za ta kasance ta haɗin gwiwa tsakanin Dangote Group da hukumar zuba jari ta Habasha, za ta rika samar da ton miliyan 3 na taki a shekara bayan kammala ta.
Aikin na da nufin amfani da albarkatu don bunkasa noma, samar da ayyukan yi, da tabbatar da wadatar abinci Afrika.
Firaministan Habasha, Abiy Ahmed, ya bayyana masana’antar a matsayin alamar hadin kai da ci gaban kasa, yana mai cewa aikin ya yana da muhimmanci.
Ya ce, “Wannan aikin yana nuna jajircewar mu wajen amfani da damar da muke da ita, karfafa haɗin kai da tabbatar da zaman lafiya.”
Abiy ya ƙara da cewa, manufar gwamnatin sa ita ce ta gina Habasha mai ƙarfi da ginshikan ci gaba ta hanyar saka hannun jari cikin masana’antu da makamashi.
Alhaji Aliko Dangote ya jinjinawa gwamnatin Abiy saboda irin sauye-sauyen tattalin arziki da ta aiwatar, wanda ya sa kasar ta zama daya daga cikin wuraren masu zuba jari a Afrika.
Ya ce, “Haɗin gwiwar mu mataki ne wajen cimma burin bunƙasa masana’antu da wadatar abinci a nahiyar Afrika.”
Dangote ya ƙara da cewa, wannan shi ne karo na biyu da kamfanin sa ke zuba jari a Habasha, bayan na masana’antar siminti da ke Mugher da ke samar da ton miliyan 2.5 a shekara.
Dangote ya bayyana cewa bayan ginin kamfanin, za su faɗaɗa aikin zuwa samar da wasu nau’ukan taki kamar NPK da sauransu.
Ya ce, cikin shekaru biyar, Habasha za ta iya zama jagorar ƙasashen Afrika a fannin noma da sarrafa taki.
Dangote ya kuma bayyana cewa wannan aikin zai taimaka wajen rage dogaro da shigo da kayayyaki daga ƙasashen waje, tare da ƙarfafa masana’antar cikin gida.
Ya bayyana godiya ga cibiyoyin kuɗi kamar Afreximbank, Africa Finance Corporation, bankunan Access, First Bank da Zenith bisa tallafin su wajen aiwatar da aikin.
Shugaban Cibiyar Musayar Kuɗi ta Nijeriya (NGX), Dr Umaru Kwairanga, ya yaba wa shugabannin ƙasar Habasha saboda ci gaban tattalin arzikin da suke samu, ya kuma bayyana fatansa game da ƙara danƙon zumunci tsakanin Nijeriya da Habasha.
Kwairanga ya ba da wannan yabon ne a cikin jawabinsa a wani liyafar cin abinci a fadar shugaban ƙasa da aka gudanar a birnin Addis Ababa na ƙaasar Habasha ranar Juma’a.
Hakan ya faru ne a wata ziyarar aiki da ta kai a daidai lokacin da aka ƙaddamar da ginin kamfanin takin zamani na Dangote dala biliyan 3.
Shugaban NGX ya yaba da irin karimcin da gwamnatin ƙasar Habasha ta yi masa, ya kuma yaba da ƙoƙarin ƙasar wajen adana ɗimbin tarihinta yayin da take gudanar da ayyukan raya ƙasa masu kawo sauyi.
“Ethiopia tana da dogon tarihi kuma abin alfahari a matsayinta na ɗaya daga cikin tsoffin ƙasashe masu cin gashin kai a Afirka.
“Na yi farin cikin ganin cewa kun adana wannan gadon yayin da kuke samar da ayyuka irin su babban madatsar ruwa ta Habasha da kamfanin siminti na Dangote, waɗanda ke a matsayin shaida mai ɗorewa ga shugabancin ku,” inji shi.
