Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Hukumar Alhazan Nijeriya (NAHCON) ta sanar da ranar 31 ga Disamba, 2025, a matsayin wa’adi na ƙarshe ga duk wanda yake son zuwa aikin Hajji a shekarar 2026 don kammala biyan kuɗin kujerarsa.
Shugaban hukumar na ƙasa, Farfaesa Abdullahi Usman, ne ya bayyana hakan a taron manema labarai da aka gudanar ranar Juma’a a birnin Kano.
Usman ya ce, an tsara wannan wa’adi ne domin tabbatar da shirye-shirye cikin lokaci da kuma gudanar da aikin Hajji cikin tsari ba tare da tangarda ba.
Ya bayyana cewa, Hukumar Jin Dadin Alhazai ta jihohi za su biya aƙalla rabon kashi 50 na kuɗin Hajji zuwa NAHCON kafin ranar 8 ga Oktoba, 2025, domin tabbatar da cewa ba a karɓe musu gurabe ba.
“Daga ranar 31 ga Disamba, dole kowane mai niyyar zuwa Hajji ya gama biyan kuɗinsa gaba ɗaya.
Waɗannan wa’adin ba matakan ofis ba ne kawai, su ne ginshiƙan da ke tabbatar da samun sansanonin kwana da wuri, kwangiloli masu ƙarfi, da kuma ingantaccen isar da ayyuka,” inji shi.
Farfaesa Usman, wanda ya dawo daga Saudiyya a ranar 22 ga Satumba, ya ce manufar ziyararsa ita ce nema da tsara mafi kyawun hidima ga alhazan Nijeriya tare da rage musu kuɗi.
“Aikinmu ya ta’allaka ne da tattaunawa, tsarawa, da tabbatar da samun mafi kyawun sabis ga alhazan Nijeriya. Kuma yau, na dawo da sakamako, ba da alkawari ba,” inji shi.
A cewarsa, ta hanyar tattaunawa mai zurfi da hukumomin Saudiyya da kwamitocin jihohi, NAHCON ta cimma ragi na sama da Naira 200,000 kan kowane alhaji.
“Da guraben mahajjata 66,910 da aka ware wa Nijeriya, hakan ya haifar da ajiyar fiye da Naira biliyan 19 ga alhazan ƙasar,” in ji Usman.
Ya ƙara da cewa, wannan nasarar ta yi daidai da shirin Shugaba Bola Tinubu na “Renewed Hope Agenda”, wanda ke nufin rage nauyin kuɗi a kan jama’a.
Hukumar ta kuma rattaba hannu kan kwangila da Kamfanin Mashariƙ Dhahabiyya don hidimar Masha’ir, da kuma Kamfanin Daleel Al-Ma’aleem don sufuri.
Usman ya ce, an kuma kammala yarjejeniya ta masauki da abinci a Madina, inda aka samo wurare masu inganci a yankin Markaziyya a farashi mai sauƙi.
Ya ƙara da cewa, NAHCON ta ƙaddamar da Kwamitin tantance kamfanonin yawon Hajji na 2026, domin tabbatar da cewa masu cancanta kawai za su halarta a aikin.
“Zamanin yin gajerun hanyoyi da watsi da ƙa’idoji ya wuce,” inji Usman.
Haka kuma ya bayyana cewa an fara horas da ma’aikata domin ƙarfafa jami’an hukumar kafin fara manyan shirye-shiryen Hajjin 2026.
