Ku ajiye kuɗinku a bankunan da CBN ya bai wa lasisi — NDIC ta gargaɗi ’yan Nijeriya

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hukumar Kula da Ajiyar Kuɗaɗe a Bankunan Kasuwancin Nijeriya (NDIC) ta gargadi ’yan Nijeriya da su tabbata cewa suna ajiye kuɗinsu ne a bankunan da Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya ba da lasisi.

Da yake jawabi a Ranar Musamman ta Hukumar a bikin kasuwanci na ƙasa da ƙasa na Abuja karo na 20, wanda ƙungiyar Kasuwanci da Masana’antu ta Abuja (ACCI) ta shirya a ranar Alhamis, Manajan Daraktan NDIC, Sunday Thompson, ya kuma shawarci ’yan ƙasa da su guji fazawa cikin tsarukan zamba (ponzi schemes).

Thompson, wanda Bimpe Akande, Daraktar Sashen Gudanar da Ayyuka ta NDIC ta wakilta, ya tabbatar wa ’yan Nijeriya cewa kuɗaɗensu suna cikin aminci a bankunan da CBN ta ba da lasisi, domin suna cikin tsarin inshorar ajiya da hukumar ke bayarwa.

Ya ce, “Wannan kulawa da taka-tsantsan abu ne mai matuƙar muhimmanci domin kare kuɗaɗen da kuka sha wahala kuka tara.

Tsawon shekaru fiye da talatin, NDIC ta taka muhimmiyar rawa wajen kare kuɗaɗen masu ajiya, musamman marasa ƙarfi, tare da ƙarfafa tsarin kuɗi na ƙasa.

Babban manufar mu ita ce inshorar ajiyar kuɗi a bankunan da aka ba da lasisi, duba harkokin cibiyoyin kuɗi, kula da bankunan da suka shiga matsala, da tabbatar da cewa ana warware matsalolin irin waɗannan bankuna cikin lumana.

Muna aiki kafaɗa da kafaɗa da CBN wajen tabbatar da daidaito da tsayayyen tsarin banki, aiwatar da dokokin banki, da kuma yin cikakken kulawa ga cibiyoyin da ke karɓar ajiya masu inshora.

Manufar mu, wacce take a ƙarƙashin taken ‘Kare ajiyar kuɗin ku a banki’, ita ce inganta haɗa kan al’umma cikin harkokin kuɗi da tabbatar da amincewar ’yan Nijeriya ga tsaron kuɗaɗensu.”

Ya ƙara da cewa, ɗaya daga cikin matakan da hukumar ta ɗauka don kare kuɗaɗen masu ajiya shi ne ƙara adadin mafi girman inshorar ajiya, domin ya faɗaɗa kariya ga bankuna daban-daban da aka ba da lasisi.

“A halin yanzu, NDIC tana inshorar masu ajiya a bankunan DMB, Mobile Money Operators, da Non-Interest Banks, har zuwa naira miliyan biyar (N5,000,000).

“Idan wani banki ya rushe, masu ajiya da ke da kuɗi sama da adadin inshorar da aka ƙayyade za su fara karɓar kuɗi har zuwa mafi girman adadin da inshora ta rufe.

By ukarofi