Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Kungiyar da ke mai fafutukar yaƙi da cin hanci a Nijeriya ta SERAP ta yi kira ga gwamnonin jihohi 36 da ministan Abuja, Nyesom Wike, su fitar da cikakken bayani kan yadda aka kashe kuɗin da ake raba musu.
Kungiyar tana buƙatar bayani ne kan kuɗin da suka samu daga asusun rarraba kuɗi na FAAC bayan cire tallafin man fetur.
SERAP ta ce an kiyasta cewa jihohi da Abuja sun karɓi kusan Naira tiriliyan 14 daga irin waɗannan kuɗi tun daga tsakiyar shekarar 2023.
Kungiyar ta ce, duk da kuɗin da suka samu amma babu wani canji da ake gani a fannin ilimi, lafiya da walwalar talakawa.
A cikin wasiƙar da ta aika ranar 4 ga Oktoban 2025, ƙungiyar ta ce akwai buƙatar gaggawa ga gwamnonin su fayyace wuraren da aka aiwatar da ayyukan da kuɗin ya tafi.
SERAP ta ce, akwai buƙatar jama’a su san yadda ake amfani da kuɗin da aka samu bayan cire tallafin man fetur.
Kungiyar ta bayyana cewa, “Akwai babban hadari na karkatar da kuɗin da aka samu daga rabon FAAC zuwa aljihun wasu mutane.”
Ta ƙara da cewa, yawancin jihohi ba su fitar da cikakken bayani ba kan yadda suke amfani da kuɗin, kuma hakan yana ci gaba da jefa talakawa cikin matsin tattalin arziki.
SERAP ta buƙaci jihohi da FCT su gayyaci hukumomin ICPC da EFCC domin sa ido a yadda ake kashe kuɗin don tabbatar da gaskiya da bin doka.
Ta ce, “Sanin gaskiya a yadda ake kashe kuɗin zai tabbatar da cewa ba a maimaita halin da talakawa ke ciki na shan wahala sau biyu – na cire tallafi da rashin amfanin kuɗin ba.”
ƙungiyar ta gargaɗi gwamnonin cewa za ta kai ƙara kotu idan ba su bi umarninta ba cikin kwanaki bakwai bayan karɓar wasiƙar.
ƙungiyar ta ce, duk da ƙaruwar kuɗin da ake rabawa jihohi a FAAC, miliyoyin ‘yan Nijeriya har yanzu suna fama da talauci, rashin albashi da rashin samun ayyukan gwamnati.
Ta bayyana cewa, “Ma’aikata a jihohi da dama suna ci gaba da bin gwamnati bashi, yayin da wasu ke kashe kuɗi wajen sayen motocin alfarma da yawon ƙasashen waje.”
