Badaƙalar Nnaji: Da na gaba ake ganin zurfun ruwa – Atiku ya buƙaci a yi bincike kan takardun karatun Tinubu da ministocinsa

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya zargi gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da kafa tsarin bogi da yaudara a cikin gwamnati, bayan murabus ɗin tsohon Ministan ƙirƙire-ƙirƙire, Kimiyya da Fasaha, Uche Nnaji, saboda cece-kuce kan takardun karatunsa.

A cikin wata sanarwa da Atiku ya fitar a Abuja ranar Talata, ya bayyana murabus ɗin Nnaji a matsayin “abin kunya ga ƙasa,” yana mai cewa hakan alama ce ta lalacewar ɗabi’a a cikin gwamnati mai ci.

Atiku, wanda ya riƙe muƙamin Mataimakin Shugaban ƙasa daga 1999 zuwa 2007, ya ce saƙe-saƙe da jabu sun zama ruwan dare a wannan gwamnati, yana mai cewa hakan na nuna halayen shugabannin da ke riƙe da madafun iko.

Ya soki yadda gwamnati ta “ƙoƙarta ɓoye abin kunya” ta hanyar barin Nnaji ya yi murabus cikin natsuwa, maimakon a kore shi kuma a gurfanar da shi gaban kotu.

“Abin da ya kamata ya zama abin kunya ga aasa, yanzu an mayar da shi kamar murabus ne na ƙashin kai. Wannan wata hanya ce ta ɓoye wani sabon abin kunya da ke nuna irin halin jabu da wannan gwamnati ke ciki,” in ji Atiku.

Ya ƙara da cewa, “Uche Nnaji bai kamata a bar shi ya yi murabus ba — ya kamata a kori shi tare da gurfanar da shi saboda yaudara da ƙirƙirar takardu.”

Tsohon ministan ya yi murabus ne ranar Talata bayan samun matsala da takardar digiri da ta NYSC, inda ake zargin jami’ar da ya ce ya kammala karatu, Jami’ar Nijeriya Nsukka (UNN), ta kasa tabbatar da sahihancinsu.

Shugaba Tinubu ya karɓi murabus ɗin nasa tare da yi masa godiya da fatan alheri.

Atiku ya kuma zargi Hukumar Tsaro ta DSS da gazawa wajen yin bincike kafin amincewa da naɗin Nnaji, yana mamakin yadda ita ce ta ƙi amincewa da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, amma ta yarda da Nnaji duk da rashin daidaito a takardunsa.

“Abin kunya ne cewa wannan ita ce DSS ɗin da ta hana El-Rufai saboda tsaro, amma ita ce ta amince da Uche Nnaji. Wannan gazawa ta sa Nijeriya zama abin dariya a idon duniya,” inji Atiku.

Ya ce, matsalar gaskiya da amana a cikin gwamnati ta samo asali ne daga sama — daga Shugaba Tinubu kansa, wanda har yanzu ake tambaya kan shekarunsa, asali, da takardun karatunsa.

“Tun daga batun Jami’ar Chicago zuwa rantsuwar bogi, an ga hujjojin cewa mutumin da ke jagorantar ƙasar nan yana da rikice-rikicen da ba a warware ba game da takardunsa,” in ji shi.

Atiku ya buƙaci gwamnati ta ƙaddamar da bincike mai zaman kansa da gaskiya kan takardun karatu da na aiki na dukkan ministoci da jami’an gwamnati — tare da farawa daga Shugaba Tinubu kansa.

“Ina kira da a gudanar da bincike mai gaskiya da cikakken bayani kan takardun karatu da ƙwarewar dukkan ministocin gwamnati, tun daga Shugaba Bola Ahmed Tinubu. ’Yan Nijeriya na da haƙƙin sanin gaskiyar waɗanda ke mulkinsu,” inji Atiku.

By ukarofi