An yi walimar haddar Alƙur’ani na ɗalibai 21 na makarantar Tarteelil ƙur’an Wattajweed

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Madarasatul Tarteelil  ƙur’an Wattajweed dake kusa da Almuntada masallacin ɗorayi na Marigayi Sheikh Ja’afar ta gudanar da walimar haddar Al’ƙur’ani mai girma na ɗalibai 21 karo na biyar a ɗakin taro na yaye ɗalibai dake sabuwar Jami’ar Bayero ranar Lahadi.

A jawabinsa shugaban cibiyar ƙur’ani na Jami’ar Bayero Farfesa Ahmad Murtala wanda Dakta Ibrahim Ahmad Indabawa ya wakilta ya ce idan aka yi duba da ƙanƙantar shekarun ɗalibai da suka yi haddar, al’umma na da ƙarfin gwiwar gaba za ta yi kyau a tsakanin matasa masu tasowa. 

Ya yi kira ga mahaddatan kan suyi ƙoƙarin ɗabbaƙa ƙur’ani sannan ya taya  iyayen yaran murna  da suka sasu a makarantar ƙur’ani da hadda a wannan yanayi da mutane suka fi karkata da son abin duniya.

Dakta Ibrahim Ahmad Indabawa ya ja hankalin iyayen ɗalibai su riƙa bada kulawa ga malamai da makarantar su riƙa ziyara lokaci zuwa lokaci. Ya nuna damuwa akan mafi yawan iyaye ba sa kai ziyara a irin waɗannan makarantu da hakan bai kamata ba, domin ziyarar za ta ƙarawa malaman makarantar ƙwarin gwiwa.

A saƙon shugaban Jami’ar Bayero Farfesa Haruna Musa ya taya waɗanda Allah ya azurta da haddar ƙur’ani murna da yi wa iyayensu fatan alheri da kulawa da karatun yaran. Ya kuma  yaba wa malaman makarantar da suka tsayu wajen karantar da ‘ya’yan musulmi haddar ƙur’ani. 

Daraktan makarantar Malam Abubakar Aminu Tafida da ya fi shahara da “Malam Siddik” ya ce taron na walimar taya murna ne ga ɗalibai 21 da sukayi hadda, wanda kuma taron shine karo na biyar tun kafa makarantar.

Ya ƙara da cewa an kafa makarantar ne a 2011 ta soma da ɗalibai da basu kai 20 ba da malamai biyu, amma yanzu cikin ikon Allah suna da ɗalibai sama da 300 da malamai 23 suna kuma da kyakkyawan dangantaka da iyayen yara  suna basu gudummuwa na abinda makaranta ke buƙata na zuwan yara da kiyaye dokoki da biyan kuɗin makaranta.

Daraktan makarantar Tarteelil ƙur’an Wattajweed ya ƙara da cewa suna bada muhimmanci ga tarbiyya da bada ingantaccen ilimi, ba a sakaci da su a tafiyar makarantar sai dai ya nuna damuwa kan yadda wasu iyaye ke janye ‘ya’yansu saboda wani buri na ilimin duniya da ake so su goge ko yanayin rayuwa, bayan makarantar ta ɗora su akan tsari da za su yi hadda.

Malam Abubakar Aminu Tafida ya ja hankalin iyaye da cewa idan suka tsayawa ya’yansu suka haddace ƙur’ani Allah zai hidimta musu da alkhairi  mai yawa  ya kuma nuna matuƙar farin cikinsa  bisa karramawa da iyayen ɗalibai sukayi masa a walimar.  

A yayin taron walimar dai an raba kyautuka ga ɗalibai da suka fi nuna hazaƙa da naɗa gwarazan shekara  na ƙur’ani na makarantar ɗaya a ɓangaren mata ɗaya daga ɓangaren maza, makarantar ta gabatar da bayar da tallafin yin karatu ga wasu ɗaliban makarantar da wasu daga malamai.

By ukarofi