Yadda Nijeriya ta tafka asarar biliyoyin Naira a lokacin yajin aikin PENGASSAN – NNPCL

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Yajin aikin na ƙasa da ƙungiyar ma’aikatan man fetur ta Nijeriya suka shiga a faɗin Nijeriya ya jawo wa ƙasar nan asarar gangar man fetur 200,000 a kowacce rana wanda hakan ya shafi samar da iskar gas da wutar lantarki.

Shugaban kamfanin man NNPC na ƙasa, Bayo Ojulari, ne yasa sanar da hakan a ranar Litinin bayan kammala wani zama da shugaban ƙasa Bola Tinubu a gidan gwamnati da ke Abuja.

“Mun rasa sama da ganga 200,000 a kullum na ɗanyen mai. Haka kuma mun samu tsaiko wajen samar da iskar gas. Haka ma abin ya shafi samar da wutar lantarki,” inji Mista Ojulari wanda ya shaida wa ‘yan jarida hakan.

A mafi matsakaicin farashi, ana sayar da kowacce gangar mai ce a kan Dala 66 wanda hakan ke nufin Nijeriya ta yi asarar kusan Dala miliyan 39.6 (Naira biliyan 57.4) na kuɗin ɗanyen man fetur a cikin kwana uku.

Blueprint Manhaja ta rawaito yadda FENGASSAN, ƙungiyar dillan man fetur ɗin ta shiga yajin aiki domin nuna rashin amincewarta da korar ‘ya’yanta da matatar man ɗangote ta yi. Sai dai a ranar Larabar da ta gabata ta janye yajin aikin biyo bayan sa baki da gwamnatin tarayya ta yi.

Matatar man ɗangote a kwanakin baya ne ta sanar da sallamar ma’aikata kusan 800 saboda zargin cin dunduniyar matatar wanda barazana ce ga kamfanin wajen gudanar da ayyukansa na tace gangar mai 650,000 a kullum.

A cikin wata wasiƙa da Femi Adekunle, jami’in kula da ma’aiikata na rukunin kamfanonin ɗangote ya fitar, ya bayyana wa ma’aikatan da abin ya shafa matsayar kamfanin na sallamar su daga aiki daga rananr 25 ga watan Satumba.

“Wannan mataki ne da ya zama wajibi domin kare matatar daga masu ƙoƙarin yi mata zagon ƙasa wajen gudanar da ayyukanta.”

A nata ɓangaren kuma PENGASSAN ta ce matatar ta sallami ma’aikatan ne saboda kawai sun zaɓi shiga ƙungiyar a hukumance.

Daga nan ta yi zargin cewa kamfanin na ƙoƙarin maye gurbin ma’aikatan da wasu da ba ‘yan ƙasa ba.

Daga nan ne ƙungiyar ta ɗauki mataki dakatar da sayar da hada-hadar iskar gas domin nuna rashin jin daɗinta.

Matatar Dangote ta bayyana matakin da PENGASSAN ta ɗauka da haramtacce kuma ba su da ‘yancin yin katsalanda kan yarjejeniyar da kamfanin ya ƙulla da ‘yan kasuwa wajen sayar musu da mai da iskar gas.

A ranar Larabar da ta wuce ce PENGASSAN ta dakatar da yajin aikin da ta shiga bayan cimma yarjejeniya da matatar ɗangote.

By ukarofi