
DƊan akarar shugaban ƙasa na jam’iyyar adawa a ƙasar Kamaru, Issa Tchiroma Bakary, ya ayyana kansa a matsayin wanda ya yi nasara a zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar a ranar Lahadi, duk da cewa hukumomin zaɓe ba su fitar da sakamakon hukuma ba har zuwa makonni biyu masu zuwa.
Tchiroma, yayin da yake jawabi ga magoya bayansa da ’yan jarida a birnin Yaoundé a ranar Talata, ya ce ya doke shugaban ƙasa mai ci, Paul Biya, wanda ya shafe sama da shekaru 43 yana mulki.
“Ina tsaye a gabanku a matsayin sabon shugaban ƙasar Kamaru da al’ummar ƙasa suka zaɓa domin kawo sauyi, haɗin kai da ci gaba,” in ji Tchiroma.
Sai dai bai gabatar da sahihan lambobi ko sakamakon da ke tabbatar da wannan nasara ba, illa dai ya dogara ne da bayanan wakilan jam’iyyarsa daga rumfunan zaɓe daban-daban.
Shugaba Paul Biya mai shekara 92, ya dare karagar mulki tun 1982, yana daga cikin shugabannin da suka fi dadewa kan mulki a duniya.
Gwamnatinsa ba ta fitar da wata sanarwa game da ikirarin Tchiroma ba tukuna.
Doka a Kamaru ta hana kowane ɗan takara bayyana kansa a matsayin wanda ya yi nasara kafin hukumar zaɓe ta ƙasa (ELECAM) ta fitar da sakamako.
Masu sharhi sun bayyana cewa wannan matakin na Tchiroma na iya janyo hargitsi ko rikice-rikice na doka. Kungiyoyin sa ido na ƙasa da ƙasa sun bukaci a kwantar da hankali da kuma mutunta tsarin zaɓe da sakamakon da hukumomi za su bayar.
Yanzu haka, al’ummar Kamaru na jiran sakamakon zaɓen cikin damuwa da fatan ganin an samu sauyi cikin lumana da gaskiya.
