
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnan jihar Inugu, Peter Mbah ya fice daga jam’iyyar PDP tare da komawa mai mulki, wato APC.
Peter Mbah ya bayyana haka ne yayin taron manema labarai da ya shirya a gidan gwamnanatin jihar da ke birnin Inugu.
“Bayan dogon lokaci da muka ɗauka muna nazari, a yau mun yanke shawarar ficewa daga PDP tare da komawa APC”, inji shi.
Ya ce ya koma APC ne saboda kyawawan manufofin jam’iyyar da ayyukan ci-gaba da take samarwa a Nijeriya da ma jiharsa ta Inugu, kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.
Gwamnan ya bayyana cewa yana da ƙwarin-gwiwar cewa komawarsa APC za ta samar wa jihar ƙarin damanmaki da ci-gaba.
Taron ya samu halartar manyan ƴan siyasar jihar da suka haɗa da Mataimakin gwamnan jihar, Barr Ifeanyi Ossai da tsoffin gwamnonin jihar, Sullivan Chime da Rt Hon. Ifeanyi Ugwuanyi, da Tsohon Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, Cif Ken Nnamani, da tsoffin ƴan majalisar tarayya daga jihar da shugaban majalisar dokokin jihar da shugaban jam’iyyar APC na jihar, da sauran muƙarraban gwamnatinsa, kamar yadda mataimaki na musamman ga gwamnan kan yaɗa labarai, Dan Nwomeh ya wallafa a shafinsa na X.
A jiya ne wasu daga cikin kwamishinonin gwamnan suka fice daga PDP tare da komawa APC.
