Yanzu-yanzu: Tinubu ya nemi Majalisar Dattawa ta tabbatar da Amupitan a matsayin shugaban INEC da wasu naɗe-naɗen

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaba Bola Tinubu ya miƙa wa Majalisar Dattawa sunan Farfesa Joash Ojo Amupitan (SAN) domin tabbatar da shi a matsayin sabon shugaban Hukumar Zaɓe (INEC).

Tinubu, a wani saƙo da ya aika wa majalisar zuwa ga shugabanta Godswill Akpabio, ya nemi ta yi nazari a kai da kuma tabbatarwa.

Tuni Akpabio ya miƙa wa kwamitin baki ɗaya ayyukan majalisar don fara aiki akan al’amarin.

A wani ɓangare kuma, Tinubu ya nemi majalisar da ta tabbatar da Misis Ayo Omidiran a matsayin sabuwar shugabar hukumar kula da tabbatar da adalci wajen raba muƙaman gwamnati da arziƙin ƙasa (FCC) da wasu mutane 28 a muƙamin kwamishinonin tarayya.

By Babaji