
Shugaban ƙasar Madagascar, Andry Rajoelina ya tsere daga ƙasar, kamar yadda wani rahoto na kamfanin dillancin labarai na Reuters ya bayyana.
Ya kuma ambato shugaban ƴan adawa da majiyoyin soji da kuma wani jami’in diflomasiyya.
Wannan ne karo na biyu a cikin wata ɗaya da dubban matasa suka kifar da gwamnati, bayan korar gwamnatin shugaban ƙasar Nepal KP Sharma Oli.
A wani labarin kuma, Rundunar sojin ƙasar ta ce ta karɓe mulkin ƙasar.
Haka ma kamfanin dillancin labari na AFP ya ruwaito wani soja mai muƙamin Kanal na cewa sojoji sun karɓe mulki.
Kanal Michael Randrianirina, shugaban rundunar sojin da ke tsaron fadar shugaban ƙasar, ya karanta sanarwar karɓe mulkin a gidan radion ƙasar.
Yana mai cewa ”mun karɓe mulki daga yanzu”, kamar yadda ya karanta.
A ƙarshen mako ne rundunar da ke tsaron fadar shugaban ƙasar ta juya wa shugaban baya, ta hanyar shiga zanga-zangar masu neman ya sauka daga mulki, wata ƴan Gen Z.
