Sarki Sanusi II ya halarci taron ƙungiyar Injiniyoyi ta duniya a China

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Mai Martaba Sarkin Kano, Khalifa Muhammad Sanusi II, ya halarci babban taron Ƙungiyar Injiniyoyi ta duniya, wato World Federation of Engineering Organizations (WFEO) 2025, da aka gudanar a birnin Shanghai, ƙasar China, a ranar Litinin, taron ya tattaro manyan masana da shugabanni daga sassan duniya domin tattaunawa kan ci gaban fasaha da injiniyanci a duniya.

An gudanar da taron ne ƙarƙashin jagorancin Shugaban WFEO na duniya, Injiniya Mustapha Shehu, wanda ɗan asalin Kano ne. Wannan ya ƙara bai wa taron armashi, duba da yadda ‘yan Najeriya, musamman ƴan Kano, ke taka muhimmiyar rawa a harkar injiniyanci a matakin ƙasa da ƙasa.

Taron ya samu halartar mataimakin shugaban ƙasar China, tare da shugabannin ƙasashe, ministoci, da fitattun masana a fannin fasaha da bunƙasa tattalin arziki. Mahalarta sun tattauna hanyoyin da injiniyanci zai taimaka wajen samar da ci gaba mai ɗorewa da sabbin hanyoyin ƙirƙire ƙirƙire domin amfanin al’umma a faɗin duniya.

By ukarofi