Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
Fitaccen ɗan kasuwa a jihar Kano, ɗansaran Kano, Alhaji Gambo Muhammad Danpass ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya akan ta ɗauki matakai na sassauta tsadar taki da manoma ke fama da shi.
Ya ce duk da cewa kayan abinci suna yin sauƙi amma kuma manoma na cikin mawuyacin hali da ba sa iya samun kuɗaɗen da za su sayi takin cikin sauƙi da hakan zai daɗa taimakawa wajen samun sauƙin rayuwa.
ɗan kasuwar na jihar Kano kuma ɗaya daga cikin dattawan Arewa, Alhaji Gambo Muhammad ɗanpass ya ƙara da jan hankalin hwamnati akan kyautata harkar tsaro da abin sai daɗa ta’azzara yake a wasu sassa musamman Arewacin ƙasar nan a ɗauki matakai da suka kamata a kyautatawa jami’an tsaro don kawar da barazanar tsaro.
Sannan ya ƙara da kira ga babban bankin ƙasa da ya sa bankuna su saki kuɗaɗe da zai yawaita a tsakanin mutane domin hakan zai daɗa haɓaka harkar sana’oi da kasuwanci maimakon dogara da ture-turen kuɗi ta waya da mafi yawan lokuta ake samun matsala.
Alhaji Gambo Muhammad ɗanpass ya yi kira ga al’ummar jihar Kano su cigaba da baiwa Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Injiniya Abba Kabir Yusuf bisa irin ayyukan cigaba da yake gudanarwa a fannoni da dama.
