* Gwamna Uba Sani ya yaba da bajinta
Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya taya Al-amin Muhammed Idris, Shugaban Kamfanin (Interface Africa) kuma ɗan asalin Jihar Kaduna, murna bisa samun nasarar zama gwarzonsa gasar ƙirƙire-ƙirƙire ta duniya ta 2025 (NeɗtGen Innoɓation Challenge) da aka gudanar a birnin Landan.
Wannan gasa ta ƙirƙire-ƙirƙire ta duniya, wadda Hukumar Ci gaban Fasaha ta Wasa ( NBTI) tare da haɗin gwiwar kamfanin ( UKALD) suka shirya, ta jawo mahalarta sama da 3,000 daga sassan Nijeriya, inda mutum 105 ne kawai suka kai ga zagaye na ƙarshe.
ƙirƙirar al’amin mai suna (Interface Africa) wani sabon tsarin fasahar makamashi ne mai tsafta wanda ke haɗa masu samar da hasken rana, masu zuba jari da masu amfani da makamashi don faɗaɗa damar samun wutar lantarki mai saukin kuɗi, ta hanyar shirinsa wacce ke da ɗimbin wakilai masu aikin samar da hasken wuta ga dubban gidaje.
An tallafawa ‘yan Kasuwa ƙanana, kuma an rage fitar da hayakin da ke gurbata muhalli a faɗin nahiyar Afirka.
Gwamna Uba Sani ya bayyana wannan nasara a matsayin babbar gagarumar bajinta da kuma abin alfahari ga Jihar Kaduna da NIjeriya baki ɗaya, yana mai jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da zuba jari a fannin kimiyya, fasaha da ƙirƙire-ƙirƙire domin bunƙasa tattalin arziki da bai wa matasa dama.
“Wannan nasara ta sake tabbatar da ƙwarewar ƙirƙira da ƙarfin tunanin matasan Jihar Kaduna. Muna gina tattalin arzikin da ke dogaro da kirkira wanda ke daraja ra’ayi tare da haɓaka baiwa” inji Gwamna Uba Sani.
“Daga ajujuwa zuwa manyan matakan duniya, matasan Kaduna suna jagorantar makomar ƙirƙire-ƙirƙiren Afirka,”
Gwamna Sani ya kuma jero wasu muhimman shirye-shirye da gyare-gyare na gwamnatinsa, kamar su Majalisar ƙirƙira da Fasaha ta Kaduna (Kaduna Innoɓation and Technology Council), Shirin Makarantun Zamani da Koyon Fasahar Zamani (Smart Schools and Digital Learning Programmes), da Kafa Cibiyoyin Koyon Sana’a da Fasaha uku a faɗin jihar Kaduna.
