
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ƙungiyar Miyetti Allah ta dakatar da shugabanninta na jihohin Bauchi, Taraba da Adamawa bisa zargin su da gazawa wajen wakiltar makiyaya da rashin kula da walwalar mambobinta.
A sanarwar da Kakakin ƙungiyar na ƙasa, Ambasada Mohammed Tasiu Suleiman ya fitar, dakatarwar ta biyo bayan ƙorafe-ƙorafen da aka samu daga mambobin ƙungiyar a jihohin da lamarin ya shafa.
Waɗanda abin ya shafa sun haɗa da Muhammad Hussaini Buzaye na Jihar Bauchi, Bammi Bello Jane na Jihar Taraba, da kuma Usman Abubakar Yirilabe na Jihar Adamawa.
Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Alhaji Abdullahi Bello Boɗejo, ya ce an ɗauki matakin ne bayan gudanar da cikakken bincike akansu.
Ya bayyana cewa, an gargadi shugabannin da aka dakatar da kada su cigaba da bayyana kansu a matsayin jagororin ƙungiyar ta kowace fuska.
Haka kuma, ya tabbatar da cewa ƙungiyar za ta cigaba da kare muradun makiyaya a dukkanin sassan Nijeriya.
