Gwamnatin Tarayya ta musanta cire JAMB a sharuɗɗan shiga jami’a da wasu makarantu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ma’aikatar Ilimi ta fitar da sanarwar da ke musanta rahotannin da ke cewa gwamnati ta cire JAMB daga cikin sharuɗɗan samun gurbin karatu a jami’o’i da sauran manyan makarantu.

Ma’aikatar ta bayyana cewa rahoton da ke yawo cewa daga yanzu ɗalibai za su riƙa samun gurbi a jami’a ba tare da JAMB ba ƙarya ne da aka ƙirƙira.

Hukumar JAMB a ɗaya ɓangaren, ta nanata cewa tana nan a matsayin hukumar da ke da hurumin gudanar da jarrabawar shiga makarantu, kuma har yanzu ɗalibai suna buƙatar shaidar UTME domin neman gurbi a manyan makarantu.

Don haka, ta yi kira ga al’umma da su ƙaurace wa labaran ƙaryar da ake yaɗawa domin ruɗar da su da ƴaƴansu.

A wani labarin kuwa, Gwamnatin Tarayya ta sanar da wani sabon tsarin shigar ɗalibai zuwa jami’o’i da sauran manyan makarantu a Nijeriya.

A cewar Ma’aikatar Ilimin, gwamnati ta sassauta wasu sharuɗɗan da ake buƙata kafin ɗalibi ya shiga jami’a, inda aka cire wajabcin samun kiredit a darasin Lissafi ga ɗaliban kimiyyar zamantakewa wato Social Sciences ko kuma Arts and Humanities yayin neman gurbin karatu.

Saidai, duk da jita-jitar da ke yawo a wasu kafafen yaɗa labarai cewa “ba sai da JAMB ba mutum zai shiga jami’a”, wannan batu ne da babu wata sanarwa a hukumance daga gwamnati ko JAMB da ke tabbatar da haka.

By Babaji