An sace wayar kwamishinan tsaro a taron tsaro na Kaduna

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

An zargi wani ɓarawo da sace wayar salular Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kaduna, Barista Sule Shu’aibu (SAN).

Al’amarin ya faru ne a yayin wani taro da ke da alaƙa da harkar tsaro a Kaduna, ranar Alhamis.

Rahotanni sun bayyana cewa al’amarin ya auku ne a yayin da jama’a suka taru a wajen, lamarin da ya jefa alamar tambaya duk da matakan tsaro masu tsauri da aka ɗauka wajen ba taron kariya.

Zuwa lokacin kammala haɗa rahoton, ba a samu bayani akan wanda ake zargin ba.

Haka kuma, hukumomin jihar ba su fitar da wani saƙo akan lamarin ba.

By Babaji