
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ofishin Jakadancin Amurka a Abuja, ya fitar da saƙon gargaɗin tsaro ga al’umma akan gangamin ‘#FreeNnamdiKanuNow’ don fafutukar sako Shugaban ƴan fafatukar kafa ƙasar Biafara (IPOB), Nnamdi Kanu.
An shirya gudanar da zanga-zangar ne a ranar Litinin, 20 ga watan nan na Oktoba a Birnin Tarayya Abuja.
Ɗan gwagwarmaya kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Omoyele Sowore ya sanar da gangamin, wanda ake tsammani zai tara dandazon mutane a yankin Eagles Square da Central Area na birnin, inda kuma akwai yiwuwar a yi tattaki zuwa Fadar Shugaban Ƙasa.
A ranar 9 ga watan Oktoba, Sowore ya sanar da zanga-zangar ta shafinsa na X, inda ya ce za su yi gangamin lumana da nufin a sako Nnamdi Kanu.
A wata takarda daga ofishin jakadancin Amurka a yau Juma’a, an ankarar da al’umma cewa gangamin ka iya haddasa rufe wasu titina, cinkoson ababen hawa, da kuma arangama tsakanin masu zanga-zanga da jami’an tsaro.
Akan haka me ofishin ya shawarci Amurkawa da ke Nijeriya da su guji yankunan da ake zanga-zanga, taƙaice zirga-zirga da ƙara matakin kulawa yayin zanga-zangar.
