‘Yan bindiga sun kai hari a Kankiya duk da sulhun da aka yi da su a yankunan Jihar Katsina

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Dandazon ’yan bindiga kimanin 100 a kan babura sun kai hari a yankin Kankiya da ke Jihar Katsina inda suka halaka mutum ɗaya tare da jikkata wasu da dama.

Shaidu sun ce ’yan bindiga sun kai harin a yankin Kwadawa da ke Gundumar Gashi da ke ƙaramar Hukumar Kankiya, inda ake Ana zargin maharan sun kai harin ɗaukar fansa ne.

Maharan da suka kai farmaki a yankin da ke Gabahsin ƙaramar hukumar, sun sace dabbobi da ba a san adadinsu ba, suna masu barazanar halaka duk mutanen yankin.

Wakilinmu ya ruwaito cewa a halin yanzu mazauna yankunan Bogga, Taiba Badole, Arahiya, Kwandawa, Rumawa, Gangara da Rugar Bindo da ke gundumar Gachi da kuma Fakuwa/Kafindangi suna yin ƙaura domin tsira da rayuwarsu.

Wani ganau ya ce’yan bindigar suna kutsawa zuwa yankunan da a baya suke zauna cikin aminci, kamar Kankiya , Charanchi, Kusada da a baya ba sa fama da matsalar tsaro.

Kazalika mazauna ƙauyukan Tama da Dokaji da ke ƙaramar Hukumar Bindawa sun bayyana fargabarsu da bayan samun labarin harin na Kankiya,  mai makwabtaka da su.

Haladu Badole ya ce, “Kimanin kwanaki uku ke nan da muka lura da wasy bakin fuska a yankunanmu, kuma a daren jiya sun kai hari suka sace dabbobin mutane.”

Mazauna yankin sun yi kira ga hukumomi da su gaggauta tura jami’an tsaro zuwa yankin domin samar da tsaro.

A baya yankin Gabashin Karamar Hukumar Kankiya ya kasance cikin amici duk da ’yan hare-haren da aka samu a yankunan Rimaye, Magam, Sukuntuni, Gyaza daKunduru da ke karamar hukumar.

Wakilinmu ya tuntuɓi kakakin ’yan sandan jihar, amma ya bayyana masa cewa suna gudanar da bincike domin gano haƙiƙanin halin da ake ciki.

By ukarofi